Kwanannan sojoji za su ceto ’yan matan Dapchi-Minista

  Dalibai ’yan mata 110 na Dapchi da ’yan boko haram suka sace kwanannan za su samu ’yanci yayin da sojoji suke daf da kwato su.   Ministan Tsaro, Mansur Dan-Ali ne ya bayar da tabbacin a ranar Asabar yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin gidan Talabijin na Chennels.   “Zai […]

Kwanannan sojoji za su ceto ’yan matan Dapchi-Minista

 
Dalibai ’yan mata 110 na Dapchi da ’yan boko haram suka sace kwanannan za su samu ’yanci yayin da sojoji suke daf da kwato su.
 
Ministan Tsaro, Mansur Dan-Ali ne ya bayar da tabbacin a ranar Asabar yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin gidan Talabijin na Chennels.
 
“Zai iya kasancewa ta yiwu cikin wannan mako, ta yiwu cikin mako biyu amma muna kan a bin kuma ina gaya muku cewa muna daf da su”. Inji shi.
 
Masu tayar da kayar bayan sun mamaye makarantar gwamnati ta kimiyya da fasaha ta GGSTC, Dapchi a jihar Yobe a ranar 19 ga watan Fabarairu inda suka sace daliban.