Kwanannan za mu gyara matatun mai-Baru
Shugaban kamfanin mai na NNPC, Dokta Maikanti Baru ya ce kamfanin ba zai yi kasa a gwiwa ba kan shirinta na gyara matatun man kasar hudu ta yadda za su rika aiki kamar yadda ya kamata. Dokta Baru ya bayyana haka jim kadan bayan ya karbi kyautar girmamawa a matsayin gwarzon shekara da jaridar […]
Shugaban kamfanin mai na NNPC, Dokta Maikanti Baru ya ce kamfanin ba zai yi kasa a gwiwa ba kan shirinta na gyara matatun man kasar hudu ta yadda za su rika aiki kamar yadda ya kamata.
Dokta Baru ya bayyana haka jim kadan bayan ya karbi kyautar girmamawa a matsayin gwarzon shekara da jaridar NewsDirect ta bashi a Legas.
Ya bayyana cewa yana daga cikin gyare-gyaran da ake yi, Kamfanin NNPC ya riga ya yi nisa wajen tattauna batun don gano bakin zaren ta yadda za a yi wa matatun gyara gaba daya.
Shugaban ya bayyana cewa kamfanin karkashin kulawarsa ya samu ci gaba wajen ganin an wadata kasa baki daya ba tare da wata matsala ba.