Kwanciyar hankali ke vunkasa kasuwanci da tattalin arziki – Muhamma Ammani
Wakilinmu ya samu tattaunawa da Alhaji Muhammad Muhammad Ammani, dan kasuwa mai harkar sayar da takalma da sauran kayan ado na maza da mata da ke kasuwar kantin kwari a jihar Kano, inda ya bayyana cewa tsare gaskiya da rikon amana sune tushen ci gaban kasuwanci, tare da tabbatar da cewa yanzu tattalin arzikin kasar […]

Wakilinmu ya samu tattaunawa da Alhaji Muhammad Muhammad Ammani, dan kasuwa mai harkar sayar da takalma da sauran kayan ado na maza da mata da ke kasuwar kantin kwari a jihar Kano, inda ya bayyana cewa tsare gaskiya da rikon amana sune tushen ci gaban kasuwanci, tare da tabbatar da cewa yanzu tattalin arzikin kasar nan yana bunkasa ta fannin kasuwanci da cinikayya. Ga kuma yadda hirar ta gudana:
Aminiya: Yaushe ka fara harkokin kasuwanci ganin cewa ga shi kana daga ckin fitattun ’yan kasuwa da ake da su a kasuwar kantin kwari?
Ammani: Na fara sha’awar kasuwanci tun a shekara ta 1987 lokacin da nake makaranta, inda nake bai wa wani abokina kudi yana sanyawa a cikin kasuwancinsa na takalma kafin daga bisani na yanke shawarar fara zama da kaina cikin shekara ta 1990. Amma kafin in fara kasuwanci ina kiwon dabbobi domin na dauki kiwo da muhimmanci a zaman rayuwa.
Aminiya: Tun daga wancan lokaci da ka fara kasuwanci zuwa yau, me ka fahimta kan kasuwanci da cinikayya, musamman ganin cewa yanzu al’amura sun canza?
Ammani: Kasan shi kasuwanci yana bukatar abu uku, na farko tsare gaskiya na biyu rike amana sai na uku juriya da hakuri. duk dan kasuwar da ya rike wadannan abubuwa na hakikance zai ga albarka cikin harkokinsa, domin kowa zai ji dadin hulda da shi ba tare da jin wani abu ba. Haka kuma na fahimci cewa a cikin kasuwanci ake samun rufin asiri, sannan ana samar da karin hanyoyi na ayyukan yi ga al’umma saboda yanzu rayuwa tana cikin wani yanayi marar tabbas.
Yana da kyau ’yan kasuwa su tsaya su rike amanar abokan huldarsu, kuma su sani cewa tsare gaskiya cikin harkokinsu zai jawo masu daukaka a kasuwancinsu da kuma albarka ba tare da wata matsala ba, tare da fatan cewa za mu kara kokari wajen kare mutuncin kasuwancinmu da na abokan huldarmu a kodayaushe.
Aminiya: Wace riba ka samu a kasuwancinka, musamman ganin cewa yau kana da kimanin shekaru talatin cikin kasuwanci?
Ammani: babu shakka ina godiya ga Allah madaukakin sarki wanda shi ne yake da iko kan komai, kuma ko shakka babu na samu riba mai tarin yawa tun daga fara kasuwanci na zuwa yau din nan. Ka ga dai ada haya nake biya ta kantunan da nake sayar da takalma, wanda a halibn yanzu duka na mallakesu, har ma na kara sayen wasu ina kasuwanci tare da yara na su goma sha biyu. don haka akwai rufin asiri cikin harkokin kasuwanci muddin dai an tsare gaskiya da rike amana a kodayaushe.
Aminiya: Ya ya kake kallon yanayin tattalin arzikin wannan kasa ta fuskar kasuwanci da kuma cinikayya a matsayin ka na dan kasuwa?
Ammani: Gaskiya dai kowa ya yarda cewa yanzu tattalin arzikin kasar nan yana bunkasa idan aka waiwayi yadda abin yake cikin shekaru uku da suka gabata. duk wanda yasan yanayin kasuwa a wancan lokaci zai shaida cewa yanzu kam an samu ingantuwar al’amura duba da abubuwan da suka faru na rsashin kwanciyar hankali da rashin tsaro da kuma tabarbarewar cinikayya. Na gamsu da yadda kasuwanci yake tafiya, kuma muna kara rokon Allah ya karo mana kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arziki a wannan kasa tamu mai albarka.
Aminiya: wadanne irin tsare-tsare kake da su na bunkasa kasuwancin ka a wannan kasuwa ta Kantin kwari?
Ammani: Ina da kyawawan manufofi na bunkasa harkokina na kasuwanci ta yadda za mu zamo a sahun farko wajen samar da guraben ayyukan dogaro da kai don rage yawan masu zaman saurare a cikin al’umma. Sannan za mu ci gaba da tsare gaskiya da rike amanar abokan huldar mu domin ganin kwalliya tana biyan kudin sabulu a kodayaushe.
Aminiya: Wane sako gareka ga saura ’yan kasuwa da abokan huldar ku?
Ammani: Ina kira garemu da mu ci gaba da kyautata yanayin kasuwancinmu da kuma kyautata wa abokan huldar mu domin bunkasa tattalin arzikin kasar mu. Sannan ina godiya ga gwamnatin Jihar Kano saboda kokarinta na kyautata yanayin kasuwannin mu, tare da jinjina wa shugabannin kasuwar Kantin kwari wajen jagoranci na adalci, tare da fatan Allah ya kara mana lafiya da kwanciyar hankali a wannan kasa tamu Najeriya.