Kwangen kunduge kadagon kwadago

Malam Na-Agege Kana ta hange-hange Kan kugin kwadagon shige-shige Kiwon  bujimi da nagge Mun ga kana ta kange-kange   Siyasa ka kada wa kuge Karin ladar kwadago a dage A daina karon bera da mage Kai ta maza kamar dage A yasar da rage-rage   ’Yan kwadago sun yi lage Bakuna duk a wage Ana […]

Kwangen kunduge kadagon kwadago

Kwangen kunduge kadagon kwadago

Malam Na-Agege

Kana ta hange-hange

Kan kugin kwadagon shige-shige

Kiwon  bujimi da nagge

Mun ga kana ta kange-kange

 

Siyasa ka kada wa kuge

Karin ladar kwadago a dage

A daina karon bera da mage

Kai ta maza kamar dage

A yasar da rage-rage

 

’Yan kwadago sun yi lage

Bakuna duk a wage

Ana tsimayar goge

Wasu sun fara coge

Za su jefa al’umma a sange

 

A dai shirya miyar dage-dage

Da tsuntsun miya na dabge

Kar ai mana kwange

Makaryata sun saba da kage

Cin mutuncin har da zage-zage

 

Damuwar kurda-kurdar tsiya

Dabgen damo-da-kura-da-diyya

Dundumin dama-damar duniya

Daura damarar dirkaniyya

Dokar dawainiyar danne dukiya

 

A dai yi mai yiwuwa

Don inganta rayuwa

’Yan kasa su zam morewa

Al’umma ta daina kwaruwa

Tsiraru su daina dira wawa

 

Na-Agege tuni na hango

Mui ta duba agogo

Lada da la’adar kwadago

Wuya ake so a zargo

Kiren karairayi ake so a kago

 

Za su hana shiga shago

Su hana ai wa kowa ungo

Sui ta kumbiya-kumbiya a kango

A daki su lullube da bargo

Talaka hunturu yai masa illa a bargo

 

Zabalbalar garin talge

Tukin tuwo muciya ta doge

Awon hatsi ba kwange

Gayauna mai yabanya ta burge

Ciyayin shuka duka an tsige

 

Karmamin kaya da tsittsige

Tsinin tsirrai tsiga an tsarge

Karonbattar kariya an yage

Zogala gandi an zuge

Zaburar zabari ta zabge

 

Turka-turkar tankiya

Tattakin takun tunkiya

Takarkarewar takurar turjiya

Turereniyar taraliya

Taba-ka-lashen tauniya

 

Karairayin masu mukamai

Ke haddasa daukar makamai

Sui ta waskiyar lashe amai

Ba manufa takamaimai

An fafata yaki ba jarmai

Ana ta musayar  kalamai

An rasa komai da komai

Mai na-duke ya daura dammai

Falke ya daure fama-famai

Magabta sun lashi maskin mai

 

A dai yi kintace

A kyautata hasashe

A daina kushe-kushe

Mu kiyayi waskace-waskace

Da Kyakkyawar niyya a ke dace

 

A dai yi waiwaye

Komai a yi kai waye

A takatsantsan da tawaye

Batun ingarma a kiyaye

Sai magabta su sha kaye

 

’Yan adawa ne da yarfe

Za su sa kasarmu rarrafe

Kowa ya tako a tafe

Mui karfa-karfan karfe

Mui ta sammako da sassafe

 

A farfajiyar makarantar Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya, a lokuta mabambanta mun sha nusar da hukumomin kasar nan muhimancin karin LADA DA LA’ADAR KADAGON KWADAGON DIREBOBIN ALLI,musamman don su suka fi kowane  dan kasar nan aiki mai muhimmanci, wato KOYAR DA WATSATTSAKE DA BUDA WAGAGEN LITATTAFAI. Maratabar direbobin alli dai karara take, domin kowane mukami mutum ya taka a zamanin nan kusan a iya cewa sun bayar da gagarumar gudunmuwa. Sai  dai manhajar makarantarmu mara hajijiya, ba za ta gajiya ba, wajen ganin an warware takun sakar da ake tafkawa tsakanin MALAM NA-AGEGE DA KUNGIYAR KWADAGO MASU KWAFAR KADAGON KOTO.

Lallai Gwamnatin Babanburin-huriyya ta yi hanzari wajen fasko cewa, ‘tsallen badaken fafutikar fantamawar masu laluben kadago ba sabon al’amari ba ne a kasar nan.’ Don tun daga shekarar alif sili da manuniyar kasa da ta kasa da ta kasa, zamanin da aka dawo da mulkin DAMO-DA-KURA-DIYYA ka’in a na’in, har yanzu ake ta yi ba kakkautawa, tunda kungiyar karajin karfafa kadago ta kunduge turka-turkar takun sakarta ba gudu, ba ja da baya, inda ta sa zare da gwamnati don ganin an cika mata lalita cif-cif.

Su kuwa wakilan gwamnati irin su Malam Na-Agege sai jan kafa suke ta yi, tare da musayar kalamai, har ta kai ga an kusan rasa komai da komai, wajen cimma matsaya ko ma a ce sun yi amai, sun lashe, tare da bai wa magabtan al’umma damar lasar maskin mai. Su kuwa wakilan ’yan masu laluben kadago sai sukuwar godiyar artabu suke yi, amma yakinsu ba jarmai. Watakila irin wannan tseren dodon kodi da hanzarin hawainiya ya sanya aka kasa kaiwa ga gaci. Duk yunkurin da ake ta yi ya za me wa al’ummar kasar nan tamkar sammakon bokokuwa (bubukuwa).

’Yan makarantar Dodorido, wajibinmu ne mu nusar da Haurobiyawa abin da ya dace, wato dai a yi mai yiwuwa.

Ko dai so ake a karke da KWANGEN KWADAGON NA-AGEGE.

Lallai a inganta farfajiyar Bokan Turai don tarairayar rai; a bai wa direbobin alli daukacin kayan aikin da suke bukata don saisaita karatun wasikun jakin dawa da na gida a kwakwalwar Haurobiyawa, ta yadda za a samar da zakakuran masana da za su iya bunkasa dabarbarun tattalawa da alkinta dukiyar kasa. Shi ke nan mun yi hannun riga da SIYASAR YASAR HAURO, al’amarin da ke haifar wa al’umma haure-haure da hauragiya a kasar Haurobiya. Daga nan an shawo kan kwashi-kwaraf din yi wa lalitar kasa karkaf ko a kwashe komai kakaf Akwai bukatar ganin Jami’an Asusun ilimi, musamman wadanda ke takaddama da hukuma a jam’in jama’ar jami’o’in Haurobiya, sun yi kaimi, wajen inganta tsarin zamantakewar al’umma, ta yadda za mu kauce wa zaman-tattakewa, ko kashin sha-kushe.

’Yan kwadago a yi takatsantsan da tawaye, domin tuni gari ya waye, mu rinka dubi da waiwaye, don gudun kada mu karke da zubar da hawaye; ko a zo ana ta batun waye, waye?! Jiki dai magayi bankar bukin dan Korau!