Kwankwasiya za ta dauki matakin shari’a game da harin Hawan Daushe

Jamiyyar APC Kwankwasiyya a Jihar Kano ta yi barazanar aukar matakan shari’ah akan Rundunar “Yan sandan Jihar Kano da kuma Gwamnatin Jihar Kano bisa harin da aka kai wa ‘ya’yan kungiyar Kwankwasiyyar a yayin gudanar da Hawan Daushe wanda aka yi ranar Asabar da ta gabata a Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Muhamamdu Sanusi II. […]

Kwankwasiya za ta dauki matakin shari’a game da harin Hawan Daushe

Jamiyyar APC Kwankwasiyya a Jihar Kano ta yi barazanar aukar matakan shari’ah akan Rundunar “Yan sandan Jihar Kano da kuma Gwamnatin Jihar Kano bisa harin da aka kai wa ‘ya’yan kungiyar Kwankwasiyyar a yayin gudanar da Hawan Daushe wanda aka yi ranar Asabar da ta gabata a Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Muhamamdu Sanusi II.

Rahotanni sun bayayan cewa a daidai lokacin da ake tsaka da gudanar da Hawan Daushe sai wasu mutane da ba a tantance ko su waye ba suka kaddamar da hari akan rukunin ‘ya’yan kungiyar Kwanwasiyya wadanda ke sanye da fararen riguna da jajayen huluna a wannan wurin, inda aka rika kai musu sara da makamai, lamarin da ya jawo ‘yan kwankwasiyyar suka sami raunika tare da haifar da rudani a wajen, inda sauran jama’a suka shiga neman hanyar tsira.

An dauki tsawon lokaci ana nuna wa juna yatsa tsakanin Jam’iyyar APC ta Kwankwasiyya mabiya tsohon Gwamna, Injinya Rabiu Musa Kwankwaso da kuma bangaren Gandujiyya dake biyayya ga Gwamnan mai ci, lamarin da masu fashin bakin siyasa ke ganin cewa ba zai haifar wa jihar da mai ido ba.

Da yake zantawa da manema labarai wani na hannun daman tsohon Gwamnan Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, Dokta Yunusa Adamu dangwani ya zargi Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano da wasu jami’an gwamnatin Jihar Kano da cewa su suka shirya gudanar da harin domin suna da kwararan hujjoji akan hakan.

Dokta dangwani wanda tsohon Kwamishinan Ma’aikatar Ruwa ne a lokacin gwamnatin Kwankwaso ya bayyana cewa an raunata kimanin mutane 20 a harin, wadanda har sai da abin ya kai su ga kwanciya a asibiti.

Dokta dangwani ya kara da cewa “Mutanen da aka raunatan sun hada da tsohon Sakataren gwamnati Rabi’u Sulaiman Bichi da tsofafin kwamishinoni da suka hada da Yusuf Bello Dambatta da ni Yunusa Adamu dangwani sai kuma wasu mutane da suka hada da Yahaya Musa Kwankwaso da Baba Abubakar Umar da Zainab Audu Bako da sauransu”.

A cewar Dokta Dangwani harin ya biyo bayan kalaman batanci da Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya furta makonni biyu da suka wuce a lokacin da aka gudanar da addu’oi ga Shugaban kasa Muhamamdu Buhari inda aka rawaito yana cewa “Ayyukan Kwankwasiyya a cikin Jihar Kano da kuma wasu jihohin sun zama bala’i da masifa da kuma munafunci da iskanci” a cewar Gwamnan shi kansa da kuma gwamnatinsa ba za su lamunci abubwuan da Kwankwasiyyar ke yi ba, don haka za su yi duk me yiyuwa wajen ganin sun hana Kwankwasiyyar motsi a jihar sai dai kome zai faru ya faru.

dangwani ya kuma danganta abin da ya faru da kin amincewa da uwar Jam’iyyar APC ta yi da shugabancin jamiyyar wanda gwamnatin Jihar ta tsara. “Kun san gwamnatin tana da haushin kin amincewa da uwar Jam’iyya ta kasa tabyi da tsarin shugabancin jam’iyyar da gwamantin jihar Kano ta kakaba shi ya sa suka zabi wanann hanya don su huce haushinsu akanmu.”

Sai dai Gwamnatin Jihar Kano a wata sanarwa da Kwamishinan Watsa Labarai, Kwamared Muhammad Garba ya sanya wa hannu ya jajantawa wadanda suka sami raunuka a lokacin Hawan Daushen, inda kuma ya jaddada cewa da zarar Rundunar Yan sanda ta kammala bincikenta za a hukunta duk mutumin ko kungiyar da ke da hannu a faruwar lamarin.

Har ila yau sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano tana sane da cewa akwai mutanen da ke son tayar da zaune tsaye sai dai gwamanti ba za ta nade hannunta wajen kalubalantar duk wanda zai zama barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’ummar jihar ba.

Shi ma a nasa jawabin Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano DSP Magaji Musa Majiya ya bayyana cewa a ranar Asabar a yayin hawan daushe an sami rigimar siyasa tsakanin Gandujiyya da Kwankwasiyya lamarin da ya kai sai da ‘yan sanda suka yi amfani da karfi kafin lamurra su daidaita. Ya ce tuni rundunarsu ta fara bincike kan afkuwar rigimar sai dai ta bayyana cewa ba a kama kowa game da faruwar lamarin ba.