Kwankwasiyya: Farar aniya laya
Ina daga cikin ‘yan jarida guda ashirin da Gwamnatin Jihar Kano ta gayyata daga sassan kasar nan don ta zazzagaya da su wuraren da ta aiwatar da wasu muhimman ayyukan da suke kwanzarta Birnin Kano a matsayinsa na Jalla Babbar Hausa, kuma cibiyar hada-hadar kasuwanci da karatun zamani da kuma na Muhammadiya. Abubuwan da muka […]
Ina daga cikin ‘yan jarida guda ashirin da Gwamnatin Jihar Kano ta gayyata daga sassan kasar nan don ta zazzagaya da su wuraren da ta aiwatar da wasu muhimman ayyukan da suke kwanzarta Birnin Kano a matsayinsa na Jalla Babbar Hausa, kuma cibiyar hada-hadar kasuwanci da karatun zamani da kuma na Muhammadiya. Abubuwan da muka gani da kuma wadanda muka ji sun kayatar da mu ainun, domin kuwa mun tabbatar mai kamar zuwa ne aka aika, Gwamna Kwankwaso tsayayye ne wajen yi wa jama’arsa hidindimun alheri. Wannan ne dalilin da ya sa ake masa lakabi, ana cewa da shi katafila sarkin aiki, wasu kuma daga ganinsa sai ka ji suna cewa aiki ga mai kare ka.
Ban yi mamakin gagarumar nasarar da Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ya samu ba dangane da haka, musamman ma saboda ganin an yi gwamnatocin soja da na farar hula da yawan gaske a Jihar Kano, jama’a kuma sun ga kamun ludayin kowannensu, sun kuma nakalci manufofi da dabarunsu na kawo ci gaba mai ma’ana, cikin gaggauwa, amma kwazo da jajircewar da Gwamna Rabi’u Kwankwaso ya yi cikin dan kankanen lokaci ya zame tamkar almara, domin kuwa an dade ba a ga irin haka ba tun kafuwar Jihar Kano a shekarar 1967.
Abin da kowa ke tunani game da haka shi ne dabarun da Gwamna Kwankwaso ya bi don samun wannan nasarar a fannonin raya Jihar Kano, wadanda suka daukaka matsayin al’ummar cikinta. Hakan ya nuna cewa tamkar gwamnatocin da suka gabaci tasa ba su yi wani abin kirki ba, duk kuwa da cewa su ma sun turza, sun yi iyakacin kokarinsu. Wanda duk zai gaji halifar Gwamna Kwankwaso sai ya yi da gaske kafin ya iya kwatanta dan kiris daga cikin dimbin ayyukan alherin da ya yi cikin dan kankanen lokaci.
Babu shakka Gwamna Rabi’u ya yi dukkan abubuwan da ya kamata gwamnati ta yi a fannonin ilmi da aikin gona da masana’antu da inganta harkokin kasuwanci; ya kuma mayar da hankalinsa kan nakaltar matsalolin da ke addabar wadannan fannoni, sa’annan ya dauki kwararan matakan kawar da su gaba daya don a huta da su dungurungum.
A zamaninsa ne aka yi hanyoyin sama wadanda Kanawa ba su taba hawa irin su ba, ga kuma wasu hanyoyin karkashin kasa da aka tsara don rage cunkoso da zirga-zirgan ababen hawa. Baicin haka nan kuma ya kakkafa turakun fitilun hanya a cikin Birni da Kewaye, ya kuma gina wata tashar wutar lantarki don rage dogaro akan janaretocin da ke samar masu da karfin lantarki. Ya kuma giggina gidaje da sababbin unguwanni masu kayatarwa, kamar na birnin Lantsandan.
Ya kuma tsara manufofi cikin sauki na rage karkashe kudin jama’a barkatai, ba bisa ka’ida ba, kuma a sabili da haka ya hana ma’aikatun gwamnati da sauran hukumominta shiga cikin matsalar rashin kudi na babu gaira, babu dalili. Maimakon a raja’a ga bankuna ko kamfanonin da ke hulda da kudi don ciwo bashi, yanzu dukiya ta wadatu a hannun gwamnati, kuma tana yin facaka da su don yi wa talakawa ayyukan da suka kamata, kuma a lokutan da suka dace, a wuraren da za su fi yin tasiri. A takaice dai Gwamna Kwankwaso ya hana ha’inci da ashararanci, ya kuma kawar da rashawa da cin hanci.
To amma inda aikace-aikacen Gwamna Rabi’u suka fi burgewa shi ne yadda ya dage wajen gina jama’a da kuma hakikancewa don ganin sai talaka ya ci moriyar arzikin da Buwayi Ya huwace wa jiharsa yadda ya kamata. Shi ya sa ya tsiro da wasu ma’aikatu don inganta ayyukan kyautata rayuwar jama’a da kuma wuraren horo don gyara yanayin zamantakewar al’umma da kuma dora su bisa mikakkiyar turbar shiriya, don su amfani kawunansu, jiharsu kuma ta ci moriyarsu. Dangane da haka ne ya bunkasa shirin hana mu’amala da miyagun kwayoyi da kuma kakkame ‘yan kwaya don a tsare su a wurin da za a koya masu hankali da ladabi, har sai sun koma cikin hayyacinsu; haka nan kuma ya hana barace-barace a fadin Jihar Kano, walau na kananan yara almajirai, ko manya da ke fama da wata nakasa, wadanda akan kebe su a wuri na musamman don a nuna masu galihu. Baicin haka nan kuma ya karfafa kungiyar ‘yan Karota don hana matasa aikata masha’a da badala, kuma saboda an kafa kungiyarsu bisa shimfidar adalci da kamanta gaskiya suna aikinsu ba sani, ba sabo, kuma idan sun yi kamu sai baba-ta-gani. Wannan ne ya sa ake tsoronsu fiye da dukkan jami’an tsaro da ke aiki a Jihar Kano.
A koda yaushe idanun Gwamna Rabi’u akan wannan kungiyar suke don ya kara tabbatar da cewa ‘ya’yanta ba su buge da gyangyadi ba yayin da suke kokarin hana barci. Ya umurce su cewa idan har sun danki wani mai laifin da zai yi tinkaho da wani babban jami’in gwamnati don a sake shi, to su nunka hukuncin da za su yi masa na take, ba ruwansa.
A sakamakon haka wanda duk ya yi za a yi masa, makiya zaman lafiya sun shiga taitayinsu, jama’a na murna, domin suna iya kwanciya, su yi barci har miyau na zubowa, suna ta minshari ba tare da fargabar komai ba. Dangane da haka ana iya cewa kyawawan ayyukan alherin Gwamna Rabi’u Kwankwaso sun zame farar aniyar da ta sanya jama’arsa suke amincewa da shi, hakan ne kuma ke karfafa masa gwiwa yana ta yi wa jama’arsa ayyukan alheri, kuma bisa ga dukkan alamu suna fatan zai yi ta yin gaba-gaba, kaman kwaryar roro, a rayuwarsa