Kwankwaso 2023: Ba za mu bi Shekarau PDP ba —Kawu Sumaila
Jiga-jigan da su ka rufa wa Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau baya watanni uku da suku gabata zuwa Jam’iyyar NNPP, sun ce suna nan daram a jam’iyar. Sun bayyaa cewa za su ci gaba da zama a NNPP, tare da yin biyayya ga shugabanninta da kuma takarar shugaban kasar jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa […]
Jiga-jigan da su ka rufa wa Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau baya watanni uku da suku gabata zuwa Jam’iyyar NNPP, sun ce suna nan daram a jam’iyar.
Sun bayyaa cewa za su ci gaba da zama a NNPP, tare da yin biyayya ga shugabanninta da kuma takarar shugaban kasar jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
- Yajin aikin ASUU: Rashin kwarewar Ministan Ilimi ne —Atiku
- DAGA LARABA: ‘Yan Ta’adda Na Fada A Ji A Najeriya.
Mai wakiltar Karaye da Rogo a Majalisar Tarayyya, Haruna Isah Dederi ne ya sanar da hakan bayan kammala wani taro da suka gudanar a Kano.
Ya ce taron ya biyo bayan fitar jagoransu na baya Sanata Ibrahim Shekarau zuwa jam’iyar PDP, wanda suka ce sun yi hannun riga da shi.
Shi ma dai Kawu Sumaila wanda a baya ke biyayya ga tafiyar ta Shekarau, ya jaddada mubaya’arsa ga Kwankwason, da dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar, Abba Kabir, da sauran ’yan takarar jam’iyar a zaben 2023.
Baya ga dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar, Abba Kabir Yusuf da ya halarci taron, akwai abokin takararsa Aminu Abdussalam, sai tsohon hadimin shugaban kasa a bangaren shari’a Kawu Sumaila, wand a baya ke tsagin Shekarau.
Haka kuma akwai kakakin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Abdulmumin Jibrin Kofa, da tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhassan Rurum, sai tsohon Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsare na jihar, Nura Ibrahim Dankadai.