Kwankwaso ba sa’anka ba ne a siyasance – NNPP ga Ganduje

NNPP ta ce da Kwankwaso ruwa ba sa’an kwando ba ne

Kwankwaso ba sa’anka ba ne a siyasance – NNPP ga Ganduje

Jam’iyyar NNPP ta kasa ta gargadi Shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje da cewa hawainiyarsa ta kiyayi ramar dan takararsu na Shugaban Kasa a zaben 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso.

A kwanakin baya ne dai Aminiya ta rawaito yadda Ganduje ya bukaci Kwankwaso ta ya koma jam’iyyar APC musamman ma da yanzu shi Gandujen ne yake shugabancinta.

A baya dai Ganduje ne ya yi wa Kwankwaso mataimaki lokacin da yake Gwamnan Kano, amma daga bisani dangantakarsu ta yi tsami lokacin da Gandujen ya zama Gwamna.

Sai dai yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron Kwamitin Zartarwa na NNPP na kasa, shugaban jam’iyyar na kasa, Abba Kawu Ali, ya ce ya sha mamakin ma yadda APC ta kyale mutum mai cike da alamomin tambaya ya shugabance ta.

Ya ce babu wani ma’aunin da za a iya amfani da shi wajen kwatanta Ganduje da Kwankwaso, saboda ya ce tsohon dan takarar tasu ba sa’an shugaban na APC ba ne.

“Jam’iyyarmu ta NNPP ta yi matukar taka rawar gani a zaben da ya kamata, musamman la’akari da cewa daga lokacin da Kwankwaso ya shige ta zuwa zabe ba a kai shekara daya ba, amma ta lashe zabukan ’yan majalisar tarayya da na jihohi, har ma da kujerar Gwamnan Kano,” in ji Shugaban na NNPP na kasa.

Shi ma da yake nasa tsokacin, Mai Binciken Kudi na NNPP na kasa, Ladipo Johnson, ya gargadi Ganduje da kada ya kuskura ya sake furta makamantan wadancan kalaman ko da a nan gaba.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta