Kwankwaso da Obi sun koma jam’iyyar NDC

Kwankwaso da Obi sun karɓi katin NDC ne a hedikwatar jam’iyyar tare da jagoranta, Seriake Dickson.

Kwankwaso da Obi sun koma jam’iyyar NDC

Tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya a Zaɓen 2023, Peter Obi, da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun koma jam’iyyar NDC.

Jiga-jigan adawar sun karɓi katin jam’iyar ne bayan ficewa daga jam’iyar ADC saboda abin da suka kira rikicin gida da na shari’a da suka dabaibaye ta.

Bayanai sun ce sun karɓi katin NDC ne a hedikwatar jam’iyar tare da jagoranta, Seriake Dickson.