Kwankwaso, Ganduje, APC da magoya baya
Watanni hudu ko a takaice in ce ranar 21, ga watan Agustan bara bayan tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Dokta Rabi`u Musa Kwankwso, ya mika wa mataimakinsa Dokta Abdullahi Umar Ganduje jan ragamar Jihar Kano a ranar 29-05-15, bayan sun shafe shekuru sama da 16, suna tafiyar siyasa ta kut-da-kut, a zaman gwamna da mataimakinsa […]
Watanni hudu ko a takaice in ce ranar 21, ga watan Agustan bara bayan tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Dokta Rabi`u Musa Kwankwso, ya mika wa mataimakinsa Dokta Abdullahi Umar Ganduje jan ragamar Jihar Kano a ranar 29-05-15, bayan sun shafe shekuru sama da 16, suna tafiyar siyasa ta kut-da-kut, a zaman gwamna da mataimakinsa har karo biyu 1999, zuwa 2003, da 2011, zuwa 2015, da kuma Minista da mai taimaka masa 2003, zuwa kusan 2007, a wata makala irin wannan mai taken “KO YA YA ZA TA KAYA TSAKANIN SANATA KWANKWASO DA GWAMNA GANDUJE.” Na yi tsokaci a kan irin yadda zamantakewarsu ta lami lafiya ta tsawon shekaru sama da 16, suna tare za ta dore, bayan Sanata Kwankwason ya amince Ganduje ya gaje shi, abin da shi ne na biyu irinsa da aka taba yi mataimaki ya gaji gwamnansa tun da aka dawo mulkin dimokuradiyyar a shekarar 1999, kai inda ma gwamnan ya ba wanda yake so ya gaje shi ba a karke lafiya ba, bisa tsarin siyasar yaro da ubangida. A jihar Zamfara ce a shekarar 2007, Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura ya fara mika wa mataimakinsa Alhaji Mahmud Aliyu Shinkafi da ake yi wa lakabi da MAS mulki.
Abin da ya sa na yi wancan hasashe saboda irin yadda na ga a cikin shekaru hudu da MAS ba a karke lafiya ba shi da ubangidansa Sanata Ahmed Sani, karshe ma dai raba gari aka yi, inda Sanata Yarima ya zauna cikin jam`iyyarsu ta ANPP, ya yin da Gwamna MAS da wasu daga cikin wadanda suka yarda su bi shi suka canja sheka zuwa sabuwar jam`iyyarsu ta PDP. Haka aka daina shan inuwar siyasa daya tsakanin Sanata Ali Modu Sheriff da tsohon Gwamnn Jihar Barno, marigayi Alhaji Malah Kacahallah da gwamna mai ci yanzu Alhaji Kassim Shettima, haka tarihi ya tabbatar ya zuwa yanzu tsakanin Sanata George Akume na Jihar Bunuwai da wanda ya mika wa mulki Dokta Gabreil Sussuwan, da kuma tsakanin Sanata Adamu Aleiro a Jihar Kabbi da wanda ya mika wa mulki tsohon Gwamna Alhaji Usman Nasamu dakingari. Haka aka karke tsakanin Sanata Ibrahin Saminu Turaki da tsohon Gwamna Alhaji Sule Lamido.Sai uwa uba tsakanin da da mahaifi, wato Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki da mahaifinsa marigayi Sanata Abubakar Sola Saraki a Jihar Kwara da dai sauransu. Har yanzu dai ba inda tarihi ya tabbatar da cewa, an zauna ko ana zaman lafiya tsakanin gwamnan da ya mika mulki da wanda ya mika wa mulki, amma kila a Jihar Kwara za a kafa wannan tarihin nan gaba tsakanin gwamna mai ci yanzu, Alhaji Abdulfatah Ahmed da ubangidansa Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Saraki.
A Jihar Kano tun bayan da Gwamna Ganduje ya zo kan karagar mulki, an ce nada `yan Majalisar Zartarwar jihar, wato Kwamishinoni da ya yi, ba tare da bin shawarar Sanata Kankwaso ba, ita ta fara hada su, batun da aka ce Sanata Kwankwaso ya so Gwamna Ganduje ya mayar da akasarin Kwamishinoninsa da sauran makarraban gwamnatinsa, amma in ban da Sakataren Gwamnatin Injiniya Rabi`u Sulaiman Bichi da Kwamishinan Ayyukan gona Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna Kwamishinan Ayyukan gona da Darakta Janar na harkokin yada labarai, Malam Halilu dantiye na tsohuwar Gwamnatin Kwankwaso, ba wanda Gwamna Ganduje ya bai wa wani babban mukami. Sannan sai kuma Gwamna Ganduje ya dukufa wajen nada dukkan wani wanda ya san Sanata Kwankwaso ya karya kara da shi a zamanin mulkinsa akan mukamai daban-daban. Abin da kawai zuwa yanzu Gwamna Ganduje bai yi gigin tabawa ba shi ma kuma ka ce lokaci yake jira, shi ne tsarin shugabancin jam`iyyarsu ta APC, wato shugabancin daga kan mazabu zuwa na kananan hukumomi zuwa jiha, wadanda duk shugabancin da Sanata Kwankwaso ya kafa ne tun ma kafin ya zama gwamna karo na biyu. Hatta Kwamitocin `yan biyar-biyar na kananan Hukumomin jihar 44, su da dukkan zababbun shugabannin mulki da nadaddun kansalolinsu da `yan Majalisun Dokokin kananan Hukumomin na Majalisun kananan Hukumomin magoya bayan Sanata Kwankwaso ne da ya bari a kan mulki da kuma wa`adinsu zai kare a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.
Amma dai tun da Gwamna Gandujen ya zo kan karagar mulki magoya bayan shugabannin biyu suke jifar junansu da miyagun kalamai na adawa, kai ka ce ba tushensu na siyasa daya ne ba.Shugabannin biyu sun yi ta kokarin su nuna wa magoya baya cewa suna tare, amma a gefe daya kuma kowannensu daga lokaci zuwa lokaci yana turo na kusa da shi don ya soki lamirin daya, musamman `yan siyasar nan da ake wa lakabi a Kano ‘Sojojin Baka,’ har sai da ta kai fagen Gwamna Ganduje yanzu ya rada wa magoya bayan Sanata Kwankwaso “Masu Baki da Kunu”.
Haka ake zaman doya da man ja, tsakanin shugabannin biyu da magoya bayansu, har zuwa ranar Litinin din wancan makon 14-03-16, ranar da ta zama rana ta uku da mutuwar mahaifiyar Gwamna Ganduje, Hajiya Fatima Ganduje a garin na Ganduje da ke cikin karamar Hukumar Dawakin Tofa. A wannan rana Sanata Kwankwaso ya shigo Kano a karon farko, tun bayan da ya mika wa Gwamna Ganduje mulki, da aniyar ya yi wa Gwamna Gandujen ta`aziyya. An yi zargin cewa, a wannan ziyarar ta`aziyya ce magoya bayan Sanata Kwankwaso suka ci karensu ba babbaka tun daga birnin Kano, har ya zuwa cikin kauyen na Ganduje, ta hanyar yada bakaken maganganu da zage-zage akan shi kanshi Gwamna Ganduje da gwamnatinsa, baya ga rarraba hotunan da suke dauke da Sanata Kwankwaso a zaman tallar takararsa ta neman mukamin shugaban kasa a shekarar 2019, a inuwar jam`iyyarsu ta APC, in Allah Ya kaimu.
Kwana daya da yin wannan ziyara sai shugaban jam`iyyar APC da na Kwamitin Dattawan jam`iyyar reshen Jihar Kano, Alhaji Haruna Umar Doguwa da Alhaji Audu kirare, bi da bi suka kira taron manema labarai, inda suka barranta da irin abubuwan da Sanata Kwankwaso da magoya bayansa suka yi a lokacin ziyarar ta`aziyyar, suna barazanar za su dauki matakin ladabtarwa a kan Sanata Kwankwaso. Nan da nan sai magoya bayan Sanata Kwankwaso a karkashin jagorancin tsohon Kwamishinan Albarkatun Ruwa na jihar Dokta Yunusa Adamu dangwani suka mayar da martini, inda suke nesanta Sanata Kwankwaso da wadancan zarge-zarge, har suna cewa ya kamata Gwamnatin Ganduje ta mayar da hankalinta a kan ayyukan da za su kyautatta rayuwar al`umma. Wannan ta sanya awoyi 24, bayan wancan taro, Shugaban Jam`iyyar APC din Alhaji Doguwa, ya sake kirawo taron manema labarai, inda ya lashe amansa a kan matsayin Kwamitin Zartarwar, wanda su kuma sauran `yan Kwamitin Zartarwar jam`iyyar suka kira nasu taron manema labaran, inda suka barranta da janye wancan matsayi da ya yi, suka kuma jaddada cewa, ba-gudu-ba-ja-da-baya Kwamitin Zartarwar yana nan akan wancan matsayi na farko da ya dauka a kan rashin da`ar da Sanata Kwankwaso ya nuna.
A takice mai karatu sa-in-sa din da ake ciki ke nan a Jihar Kano tsakani Sanata Kwankwaso da Gwamna Ganduje da Jam`iyyar APC da magoya baya, idan dai ba Allah Ya kiyaye ba, to kuwa ba abin da zai hana ruwan siyasar ubangida da yaron gida ya daya daga cikinsu, kamar yadda ta bayyana a wasu jihohi yanzu a kasr nan. Yadda shugabannin biyu su ka iya bakinsu da jan linzamin magoya bayansu nan gaba shi kadai zai hana rabuwa ta siyasa tsakanin shugabannin biyu na siyasar jihar Kano, samuwar haka kuma zai yi matukar wuya, musamman daga magoya baya da akasari da rashin zaman lafiyar manya suke samu.