Kwankwaso: Kama-karya ko adalci da gaskiya?

Da an ambaci mai mulkin kama karya, ba abin da yake zuwa zucyar jama’a sai ga wani shugaba da mai gallaza wa mutanensa. To amma a mulki irirn na dimokuradiyya sauda yawa ’yan adawa sukan yawaita amfani da wnnan kalma ta kama karya ga abokin adawar su da yake a kan mulki, musamman ma idan […]

Kwankwaso: Kama-karya ko adalci da gaskiya?
Kwankwaso: Kama-karya ko adalci da gaskiya?

Da an ambaci mai mulkin kama karya, ba abin da yake zuwa zucyar jama’a sai ga wani shugaba da mai gallaza wa mutanensa. To amma a mulki irirn na dimokuradiyya sauda yawa ’yan adawa sukan yawaita amfani da wnnan kalma ta kama karya ga abokin adawar su da yake a kan mulki, musamman ma idan wannan shugaba ba ya saurara wa rashin gaskiya kowa  kuwa ta shafa. Wannan shi ne yake faruwa yanzu a Kano. Ganin irrin yadda Gwamnan Kano  ya tsaya kai da fata don a tsayar da gaskiya a mulkin sa, kuma ba ya shakkar kowa ya yi rashin gaskiya, shi ne yasa  ’yan adawa suke cewa yana mulkin kama karya. Wanan hali na ‘yan adawa ba sabon abu ba ne  Don kuwa a kwai misalai da yawa a duniya, inda wasu shugabanni da suka jajirce don tabbatar da gakiya, ’yan adawa suke kiransu masu mulkin kama karya. Kuma abin lura a nan, shi ne, wadannan shugabanni sun ciyar da kasar su gaba nesa ba kusa ba.
Da farko dai bara mu dauki Shugaban kasar Turkiyya, wato, Raceb Tayyeb Erdogan. Lokacin da ya zama Shugaban kasar Turkiyya, tana cikin matsaloli sosai. Domin kuwa tattalin arzikinsu yana ciki mawuyacin hali.Mutane ba aikin yi; farashin kaya yana ta tashi; masana’antu suna rufewa. To amma da shugaban ya toshe kunnesa ,ya kama aiki gadan-gadan, kuma tabbatar da mutane suna aiki da gaskiya da bin doka, cikin sauri sai ga shi kasar ta canza. A halin yanzu Turkiyya tana daya  daga cikin kasashen da tattalin arzinkin su ya fi bunkasa a duniya. To, amma wannan hali na rashin saurara wa marasa gaskiya, yasa ‘yan adawa suna kiran shugaban mai mulkin kama-karya.
Misali na biyu shi ne na kasar Rwanda. Lokaci da Paul  Kagame ya amshi ragamar kasar, ya tarar da ita a rarrabe, bayan kisan kiyashin da ‘yan hutu suka yi wa ‘yan tutsi. Kuma, kusan komai ya tsaya cik. To amma da shugaban ya tsaya kyam don tabbatar da gaskiya a cikin gwamnati, nan da nan sai abubuwa suka canza. Ya bullo da shirye shirye da yawa. Kuma ya nuna ba sani, ba sabo. Wannan jajirce wa tashi tasa yanzu kasar ta ci gaba. A hanlin yan zu ma tana daya daga cikin kasashen da tattalin arzikinsu ya fi bunkasa cikin sauri a Afirka; kwanaki ma wata kungiya ta auna cigaban biranen duniya, ta ce, babba birnin kasar, wato, Kigali, yana daya daga cikin wadanda suka fi zaman lafiya a duniya. To, amma shi ma, kamar takwaransa na Turkiyya ‘yan adawar kasar suna cewa yana mulkin kama karya.
Wadannan misalai sun nuna cewar ashe ba sabon abu ba ne ganin yadda ‘yan adawa suke cewa Gamna Rabi’u Musa  Kwankwaso yana mulkin kama karya.
Kowa ya sani cewar Jihar Kano ba ta taba samun cigaba cikin gaggawa ba kamar zamanin wannan mulkin na Kwankwaso. Wannan kuwa ya faru ne saboda irrin jajircewarsa kamar yadda wadancan shugabanni da na ambata abaya suka yi.
Kano a yanzu ta zama gagara misali. Komai sai Ala sambarka. Dokoki na aiki sosai ba kamar a baya ba. Ko ta fuskar ilimi kawai muka dauka mun san cewar a karkashn Kwankwaso ta dar ma sa’a. Domin ko a ’yan shekaru masu zuwa ina ganin Kano ce za ta rika bai wa makwabta kwararru; kamar likitoci da injiniyoyi da unguwar zomoda masu hada magunguna. Wannan ko zai faru ne saboda irin tsari da gwamnana yayi. Kuma halin sa na ba sani, ba sabo, in dai ga aikin gwamnati ne, shi ne ya samar da wadannan nasarori. Kuma wannan hali nasa shi ne ‘yan adawa suke kira mulkin kamakarya. Idan haka mulkin kama karya yake da amfani, to, ina ganin ba laifi ba ne, don shugaba ya yi irin wannan mulkin.  
Yunus Ahmed  Kabo, ya rubuto ne daga Mazabar Kabo, Jihar Kano.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya