Kwankwaso na barazanar ficewa daga PDP
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar PDP idan har jam’iyyar ta cire sunan wani dan takara wanda yake mamba daga cikin ayarin ‘yan Kwankwansiyya. Yayin zaben fidda gwanin ‘yan takarar, Kwankwaso dai yana da ‘yan takara dake neman mukamai dabandaban, wanda ake tunanin sun kai ga nasara ne […]
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar PDP idan har jam’iyyar ta cire sunan wani dan takara wanda yake mamba daga cikin ayarin ‘yan Kwankwansiyya.
Yayin zaben fidda gwanin ‘yan takarar, Kwankwaso dai yana da ‘yan takara dake neman mukamai dabandaban, wanda ake tunanin sun kai ga nasara ne saboda zabin Shugaban Kwankwasiyyan.
Majiyar mu ta gano cewa, tsohon Gwamnan ya gargadi jam’iyyar ne lokacin wata ganawar da aka yi a dakin taro na Legacy House a Abuja.