Kwankwaso na zawarcin Doguwa zuwa NNPP

Jam’iyyar NNPP na zawarcin Alhassan Ado Doguwa ya dawo cikinta

Kwankwaso na zawarcin Doguwa zuwa NNPP

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

Jam’iyyar NNPP ta fara zawarcin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya, Alhassan Ado Doguwa, a Jihar Kano.

Shugaban NNPP na Kasa kuma dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kafa kwamitin sulhu da Doguwa domin ya dawo NNPP.

Hakan kuwa na zuwa ne bayan rikicin cikin gida da ya barke a Jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Kano, tsakanin Doguwa da mataimakin dan takarar gwamnan jihar, Murtala Sule Garo.

A yayin da NNPP ke zawarcin Doguwa, Shugaban APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbbas, a wani sakon murya ranar Litinin, ya ce an dinke barakar, kuma Garo da Doguwa sun yafe wa juna abin da ya faru tsakaninsu.

Ana cikin haka ne Aminiya ta samu rahoto cewa Kwankwaso, tsohon uban gidan Doguwa, yana neman jawo shi zuwa NNPP bayan dan majalisar ya nuna shirinsa na su sasanta.

A ranar Juma’a, Doguwa da magoya bayansa sun yi jirwaye da kamar wanka game da shirinsu na sake hadewa da Kwankwaso; muddin ya kira shi ko ya turo wakilcin mutum biyu su yi mishi ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa.

Duk da cewa bai ce ya bar APC ba, ya yaba da kwarewar siyasar Kwankwaso da kuma shirinsa na su sasanta idan tsohon uban gidan nasa ya nemi hakan.

Kwankwaso ya amsa bukatar Doguwa

Da yake tabbatar da zawarcin da NNPP ke wa Doguwa a ranar Lahadi, dan majalisar mai wakilatar Rano/Bunkure/Kibiya, Kabiru Alhassan Rurum, ya ce Kwankwaso ya amince da bukatar Doguwa har ya kafa kwamitin sulhu mai mutum hudu da zai je masa ta’azziyya nan ba da jimawa ba.

Rurum, tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano ne da ya sauya sheka daga APC zuwa NNPP ya ce, “Sanata Rufa’i Sani Hanga ke jagorantar kwamitin wanda ni da Shugaban Jam’iyyar NNNP na Jihar Kano, Honorabul Umar Haruna Doguwa da Honorabul Sarki Aliyu Daneji ke matsayin mambobi.

“A baya yawancinmu muna wasu jam’iyyu ne domin yakar Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, amma bayan la’akari da gogewarsa a siyasa muka biyo shi NNPP kuma ina tabbatar maka yanzu mun fi samun nutsuwa.

“Ina ba wa Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar tabbacin cewa zai samu gagarumar tarba a NNPP a matsayinsa na tsohon masu uwa a gindin murhu.

“Ina magana ne da yawun Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da kuma kwamitinmu na mutum hudun; A siyasa babu aboki ko makiyi na dindindin, amma mu abota muke son ginawa ba kiyayya ba.”

Yanzu na fara sa kafar wando da Garo —Doguwa

A lokacin da yake wa magoya bayansa bayani ranar Juma’a, Doguwa ya ce shi yanzu ya fara yakar Murtala Sule Garo — wanda ya yi wankin babban bargo.

Ya kuma bayyana cewa shi ya sa a lalata hotunan Garo a matsayin ramuwar gayya kan yadda mataimakin dan takarar gwamnan ya sa aka lalata nasa hotunan a lokacin ziyarar dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu a jihar.

Ya yi wannan jawabin ne bayan Kwamishin Yada Labarai kuma kakakin Kwamitin Yakin Neman Zaben Gawuna/Garo, wato Muhammad Garba, ya sanar cewa an sasanta su.

A sanarwar, Muhammad Garba, ya roki mambobin APC kada su bari NNPP ta yi amfani da abin da ya kira dan sabani da aka samu ta kawo rabuwar kai a APC.

Makomar Doguwa a zaben 2023

Masu nazarin siyasa dai na ganin rikicin dan majalisar da Garo na iya hana shi  komawa kan kujerarsa a zaben 2023, kamar yadda ta faru da Abdulmumin Jibrin Kofa a zaben 2019.

Sakamakon rikicin Kofa da jagororin jam’iyyar, sai suka goyi bayan abokin adawarsa kuma dan takarar jam’iyyar PDP a wancan lokaci, Ali Datti Yako, ya kayar da shi a kujerarsa ta Mazabar Tarayya ta Kiru/Bebeji.

A halin yanzu kuma, Doguwa na fuskantar babban kalubale komawa kujerarsa daga dan takarar NNPP, Air Commodore Salisu Yusha’u a zaben 2023.