Kwankwaso ya bude ofishin yakin neman zabensa a Jihar Nasarawa
Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da ofishin kamfen dinsa na takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa. Da yake jawabi a wajen bikin Gwamna Kwankwaso wanda dan majalisar Jihar Kano Alhaji Musa Adamu ya wakilta ya ce idan aka yi la’akari da halin kunci da kasar nan ta samu kanta a ciki […]
Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da ofishin kamfen dinsa na takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Da yake jawabi a wajen bikin Gwamna Kwankwaso wanda dan majalisar Jihar Kano Alhaji Musa Adamu ya wakilta ya ce idan aka yi la’akari da halin kunci da kasar nan ta samu kanta a ciki ya zame dole ya fito takarar Shugaban kasa mai zuwa don ceto kasar nan.
Ya ce kasancewa Jihar Nasarawa jiha ce ta Jam’iyyar APC ya sa ya fara bude ofishin kamfen dinsa a jihar.
Ya ce za a bude irin wannan ofishin a sauran jihohin kasar nan ba tare da bata lokaci ba, sai ya gode wa kungiyar Kwankwasiya 2015, a jihar kan gudumawa da sadaukarwa da suke yi wajen tabbatar cewa ya samu nasara a zabe mai zuwa.
Sai ya yi kira ga al’ummar jihar baki daya su tabbatar sun shiga Jam’iyyar APC su kuma kada mata kuri’unsu a zabubbuka masu zuwa don kwato ’yancinsu.
Tun farko a jawabin tshoon shugaban Jam’iyyar ACN a jihar kuma shugaban kungiyar Kwankwasiya 2015 a jihar Alhaji Alhassan Alhaji ya bayyana Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin wanda ya cancanta ya shugabancin kasar nan a zabe mai zuwa don kawo ci gaba mai ma’ana.