…Kwankwaso ya cancanci Shugabancin Najeriya – Solomon Dalung
Mai neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar APC kuma jigo a kungiyar Dattawan Arewa Barista Solomon Dalong ya ce idan aka dubi ayyukan raya kasa da Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso yake gudanarwa, ya dace a ba shi shugabancin Najeriya.Barsita Solomon Dalung ya bayyana haka ne a wurin gangamin kaddamar da […]
Mai neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar APC kuma jigo a kungiyar Dattawan Arewa Barista Solomon Dalong ya ce idan aka dubi ayyukan raya kasa da Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso yake gudanarwa, ya dace a ba shi shugabancin Najeriya.
Barsita Solomon Dalung ya bayyana haka ne a wurin gangamin kaddamar da kungiyar Kwankwasiya reshen Jihar Filato a garin Jos a ranar Asabar da ta gabata, inda ta ce idan Gwamna Kwankwaso ya zama Shugaban kasa zai magance matsalolin da ake fuskanta a Najeriya. Don haka ya yi kira ga al’ummar Nkasar nan su ba Gwamna Kwankwaso goyon baya da hadin kai domin ya shugabancin kasar nan, ya fitar da ita daga mugun halin da take ciki a yanzu.
Barista Dalung ya nuna takaici kan kashe-kashen da ke faruwa a kasar nan, inda ya ce da yardar Allah za a magance kashe-kashen da ake yi a Najeriya kuma za a hukunta dukkan masu jawo kashe kashen. Kuma ya yi kira ga Musulmi da Kirista su zauna lafiya.
Sakataren Jam’iyyar APC reshen jihar Alhaji Bashir Musa ya ce in Allah Ya yarda APC za ta kayar da PDP a zaben 2015, domin APC tana da shugabanni nagari irin su Gwamnan Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.
Ya ce duk wanda ya je Jihar Kano zai tabbatar cewa wannan bawan Allah ya yi ayyukan raya kasa masu yawa. “Mun yi imani irin abubuwan da Gwamna Kwankwaso ke yi a Jihar Kano, zai iya yin su a Najeriya baki daya. Yanzu dole ne mu yi gaskiya a Najeriya, domin an yi rashin gaskiya ba mu ga ribar da muka samu ba, sai shiga cikin matsaloli. Don haka dole ne mu yi gaskiya don mu bar wa ’ya’yanmu tarihin kirki,” inji shi..
Shugaban kungiyar Kwankwasiya reshen jihar Alhaji Nuradeen Muhammad Inuwa Maigado Takai ya ce soyayya da kuma ayyukan da Gwamna Rabi’u
Kwankwaso yake gudanarwa a Jihar Kano ne suka ba su karfin gwiwar kaddamar da kungiyar Kwankwasiya a Jihar Filato. Ya ce za su shiga kananan hukumomin Jihar Filato 17 don jawo hankalin jama’a su goyi bayan Kwankwasiya har Allah Ya kai Gwamna Kwankwaso kan kujerar Shugabancin kasar nan.