Kwankwaso ya ci zaben shugaban kasa a Kano

Kwakwaso ya samu rinjaye a 36 daga cikin kanana hukumomi 44 na Jihar Kano.

Kwankwaso ya ci zaben shugaban kasa a Kano

Sanat Rabi’u Musa Kwankwaso

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP ya lashe zaben shugaban kasa a Jihar Kano da kuri’a kusan miliyan daya.

Kwakwaso ya yi nasara ne bayan ya samu gagarumin rinjaye da kuri’a 997,278, inda ya ba wa manyan abokan hamayyarsa gagarumin tazara, kamar yadda baturen zaben kuma Shugaban Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Farfesa Lawan Suleiman Bilbis, ya sanar a ranar Litinin da dare.

Sakamakon zaben ya nuna Kwankwaso ne ya yi nasara a 36 daga cikin kananan hukumomi 44 da ke fadin Jihar Kano.

Ya bayyana cewa, wanda ya zo na biyu shi ne dan taarar Shugana kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, wanda ya samu kuri’a 517,341, wanda Kwankwaso na NNPP ya ba wa tazarar kuri’a 479,000.

Wanda ya zo na uku shi ne tsohon Mataimakin Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar na PDP da ya samu 131,604 sannan Peter Obi na LP ya tashi nda 28,522.