Kwankwaso ya ciyar da al’umma gaba
A duk lokacin da ka ga al’umma ta ci gaba to tabbas in ka yi bincike za ka ga cewar ta samu shugabanni masu hangen nesa. Kuma wadannan shugabanni suna aiki ne tare wajen tabbatar da wannan ci gaban. Kuma a nan in aka ce shugabanni, to fa ana nufin shugabanni masu mulki da ‘yan […]
A duk lokacin da ka ga al’umma ta ci gaba to tabbas in ka yi bincike za ka ga cewar ta samu shugabanni masu hangen nesa. Kuma wadannan shugabanni suna aiki ne tare wajen tabbatar da wannan ci gaban. Kuma a nan in aka ce shugabanni, to fa ana nufin shugabanni masu mulki da ‘yan kasuwa da kuma malamai na addini. Ko da mun bi tarihi, za mu ga wannan ne ya faru zamanin Sa Ahmadu Bello, Sardaunana Sakwkwato. Domin kuwa, tarihi ya nuna mana cewar, shi ya zauna da mashawarta daga bangarori daban-daban. Wannan shi yasa ya yi abubuwa masu yawa ga Arewacin kasar nan, wadanda har yanzu ake cin gajiyar su. Irin wannan hadin karfi da karfe wajen samar da ci gaban al’umma, shi ne babban dalilin kawo wa Kano ci gaba a halin yanzu. Domin kuwa, kowa ya je Kano, yasan cewar akwai shugabanci mai alkibla a kasa. Hakika, Kano ta yi sa’a da gwamna mai son ci gaban al’ummarsa, wato Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso . Domin wani abu da ya kamata mu sani, shi ne, a zamanin da muke ciki yanzu, kasashen da ke tunkahon ci gaba a duniya a yau, sun kai ga hakan ne don irin muhimmancin da suka bai wa ilmi. kasashe irin su Malesiya da Singafo da Koriya ta Kuda da dai sauransu ba su yi wasa da ilmi ba. Kuma kowa ya ga irin matsayin suka kai yanzu a duniya. To, a Kano a yau, ba a wata rana ba daban, babu lokacin da aka bai wa ilmi muhimmmanci kamar a yanzu. Kamar yadda muka sani shi ilmi abu ne mai fadi da gaske. Saboda haka da zuwan wannan Gwamna sai ya tabbatar ya kafa makarantu daban-daban, wadanda za su ba da ilmi a kan fannoni daban-daban. A Kano ba ya ga jami’o’in da ake da su guda biyu, akwai manyan makarantun ilmi fiye da 20. Wadannan makarantu kuwa sun hada da na koyon ilmin komfuta da ban-ruwa da wasanni da unguwar zoma da harkokin kiwon dabbobi da dai sauransu. Wannan tsari ne wanda babu irin shi a dukkan wata jiha ta kasar nan. Kuma wanda ba karamin ci gaba zai kawo wa Kano ba a ‘yan shekaru masu zuwa. Ganin wannan kyakykyawan shugabanci ya sa kuma har manyan ‘yan kasuwa na Kano, Kamar Alhaji Aliko Dangote, suka fara shiga harkar ci gaban Kanon. Ko da yake a matsayin sa na wanda ya fi kowa kudi a Afirika ya kamata a ce ya kara hobbasa. Amma duk da haka shi ma yana bayar da tasa gudunmawar, musamman ma a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil, da kuma samar da aikin yi ga al’umma, ta hanyar gina masana’antu daban-daban. Kuma muna fata zai dada hobbasa, kamar yadda nace a baya, ta ganin cewar ya shiga harkar samar da guraben karo ilmi ga al’umma, kamar yadda ‘yan uwansa masu kudi a duniya suke yi. Har wa yau Gwana Kwankwaso bai tsaya a nan ba, har malamai ma sai da ya janyo su a jika. Kuma wanda a halin yanzu kowa shaida ne ga irin gudun mawar da malaman addini suke bayarwa ga ci gaban Kano . Misali Sheik Aminu Ibrahim Daurawa, wannan malami ya canja al’amura da yawa a Kano. Mata da yawa sun fidda ran za su sake yin aure a rayuwarsu, bayan sun rabu da mazajen su, ko kuma mazajen nasu sun mutu. To, amma da malamim ya bada shawarar bullo da wani tsari na aurar da zawarawa. Kuma gwamnti ta amince da shi. Yanzu mata dubbai da mazajen su. Kuma wannan ya faru ne ta hanyar wannan shiri kyakykyawa. Dukkan mu musan yadda al’umma take kasan cewa in har tsarin iyalinta ya rushe. Saboda haka ne abin bai tsaya ga aurarwar kawai ba. Ganin yadda al’ummar tamu take wasa da wannan babban lamari na aure sai da malamin ya tabbatar an yi tsari, inda auren zai zama mai inganci kamar yadda addnin Musulunci ya tanada. Wannan ba karamin ci gaba ya kawo ba a Kano. Kuma shi yasa ma jihohi irin su Gwambe da Katsina da Kaduna suka fara kwaikwayar wannan tsari. A halin yanzu ma har kungiyoyi masu zaman kansu sun fara kaddamar da irin wannan tsari na aurar da zawarawa. Ana cikin haka kuma sai Allah ya kawo wa Kano sarki mai jini a jika, kuma wanda Allah ya albarkace shi da ilimin addini da na zamani, wato Sarki Muhamadu Sanusi II. Da zuwan sa, sai abubuwa suka fara canjawa. Kuma ya ci gaba da dorawa a kan ci gaban da magabatan sa suka assasa. Kwanan nan Sarki Sunusi ya bukaci a yi wata doka wadda za ta rage yadda ake sakin aure barkatai, wadda wannan wata annoba ce da ta yi yawa a cikin al’ummar Hausawa da Fulani. Kuma wannan da ma yana daya daga cikin abin da Sheik Aminu Daurawa yasa a gaba, a irin tsare-tsaren da ya ke so gwamnati ta aiwatar. Kuma ba sai an fada ba, wannan yawan sakin aure, yana daya daga cikin abin da yake lalata al’umma. Shi yasa sarki ya ga ya kamata a ce an yi wata dokar da za ta rinka hukunta duk wanda ya yi saki ba tare da ya bi matakan da addinin Musulunci ya tsara ba. Idan muka duba, kuma kamar yadda na yi tsokaci a baya wannan duk yana faruwa ne saboda samun Gwamna mai hangen nesa, kuma wanda ya ja kowa a jika, don a hadu a ga an fidda jaki daga duma. Kuma wannan ya nuna yadda dukkan bangarori sukan hadu suga al’ummar su ta ci gaba. Kuma hakika in har wadannan bangarori na Kano, wato Shugabannin siyasa da sarakuna da malamai da masu kudi suka ci gaba da irirn wannan haduwa da bada gudunmawa. Don haka Kano ta ta tsere wa sa’o’inta fintinkau wajen ci gaba. Yunus Ahmed Kabo ya rubuto makalarsa daga Kabo jihar Kano.