Kwankwaso ya dakatar da zuwa Kano gobe
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fasa zuwa Jihar Kano Gobe kamar yadda aka shirya. Tsohon Sakataren Gwamnatin jihar, Dokta Rabiu Sulaiman Bichi ne ya sanar da hakan, inda ya ce, “Kwankwaso ya fasa shigowa Kano gobe saboda kiyaye aukuwar rikicin da zai iya faruwa idan ya shigo bayan shawarwari da ya sama daga wasu masu […]
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fasa zuwa Jihar Kano Gobe kamar yadda aka shirya.
Tsohon Sakataren Gwamnatin jihar, Dokta Rabiu Sulaiman Bichi ne ya sanar da hakan, inda ya ce, “Kwankwaso ya fasa shigowa Kano gobe saboda kiyaye aukuwar rikicin da zai iya faruwa idan ya shigo bayan shawarwari da ya sama daga wasu masu kishin kasa. Saboda haka, bayan wadannan shawarwari da muka yi da kuma tuntuba mai zurfi, muna bakin cikin sanar da cewa mun dakatar da zuwa Kano na wani dan lokaci,”