Kwankwaso ya gana da Tinubu a Fadar Shugaban Kasa

Kwankwaso ne abokin hamayya na farko da ya gana da Tinubu a Fadar Shugaban Kasa.

Kwankwaso ya gana da Tinubu a Fadar Shugaban Kasa

Rabiu Musa Kwankwaso

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a Fadar Gwamnatin Najeriya da ke Abuja.

Kwankwaso shi ne abokin hamayya na farko da Shugaba Bola Tinubu ya karbi bakuncinsa bayan sun yi adawa da juna a Zaben Shugaban Kasa wanda aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Kazalika, Kwankwaso da Shugaba Tinubu sun yi makamanciyar wannan ganawa a birnin Paris na Faransa kwanaki kadan gabanin rantsar da Shugaban Kasar a ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata.

Ana iya tuna cewa Kwankwaso ne ya zo ma hudu a Babban Zaben inda ya yi takara a jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari.

Trump ya dakatar da kafar watsa labarai ta VOA

Mahaifiyar Sarkin Gwoza ta rasu

Yadda za a girka ‘Kamoniya’

An kama malama tana lalata da ɗalibinta