Kwankwaso ya gargadi ’yan majalisa kan tsige Buhari
Kwankwaso wanda tsohon Ministan Tsaro ne ya gargadi ’yan Majalisar kan zumudin neman tsige Buhari
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gargadi ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa da su yi hattara da yunkurin tsige Shugaba Buhari kan tabarbarewar tsaro.
Kwankwaso wanda tsohon Ministan Tsaro ne ya gargadi ’yan Majalisar cewa zumudin neman tsige Buhari abu ne da zai iya tayar da zaune tsaye a Najeriya.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 28 a Sakkwato
- Bincike: Shin an kashe dan bindiga mai shan jini a Jibiya?
Tsohon gwamnan Kanon, ya ce tabbas abin damuwa ne halin da Najeriya ke ciki na tabarbarewar tsaro, kuma ya kamata gwamnati yi tsayuwar daka wajen shawo kan matsalar.
Kwankwaso ya kuma bukaci gwamnati da ta kasance mai tuntubar bangarorin da ke kwararan dalilai ko koke domin ta magance su.
Ya bayyana haka ne a ganawarsa da Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, gabanin taron kaddamar da ofishin jam’iyyarsa ta NNPP a Ilori, hedikwatar jihar, da sauran sannan jihar.
A lokacin da yake karbar bakuncin Kwankwaso, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, ya shawarci ’yan siyasa da su guji sin siyasa da gaba.
Tun da farko sai da Kwankaso ya kai ziyarar ban girma ga Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari.
Tabarbarewar tsaro a Najeriya
A cikin makon nan ne ’yan jam’iyyun adawa a Majalisar Dokoki ta Kasa suka ba wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari mako shida ya magance matsalar tsaro.
Mambobin majalisar sun yi barazanar tsige shugaban kasar, muddin ya kasa magance matsalar bayan cikar wa’adin da suka ba shi.
Barazanar tasu na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro, musamman a Yankin Birnin Tarayya, ta dauki hankali.
A ranar Asabar na makon jiya ne ’yan ta’adda suka fitar da bidiyo suna barazanar sace Buhari da manyan jami’an gwamnatinsa.
Barazanar tasu na cikin bidiyon da suke duka fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da suka sace ne.
Washegari, ranar Lahadi, ’yan ta’adda sun kashe sojoji, ciki har da hafsoshi biyu daga rudunnar da ke tsaron shugaban kasa a Abuja.
An kashe sojojin ne a hanyarsu ta dawowa daga binciken sharar fage bayan ’yan ta’adda sun tura wasikar barazanar hari ga Makarantar Koyon Aikin Lauya da ke Bwari.
A ranar Lahadin ’yan bindiga sun kai wani hari a kauyen Sheda da ke makwabtaka da Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya da ke Kwali.
Harin na Kwali dai ya yi sanadiyyar rufe makarantar a ranar Litinin.
Daga bisani aka rufe ragowar makarantun da ke yankin Birnin Tarayya a ranar Laraba.