Kwankwaso ya kara kwankwatsa Lado
Tsohon Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya kara kwankwantsa Sanata Basheer Garba Lado da kasa, bayan da Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta Jihar Kano, ta yi watsi da karar da ya kai gabanta yana kalubalanta nasarar Kwankwaso a zaben da ya gabata.Sanata Bashir Garba Lado wanda ya tsaya takarar Sanatan Kano ta Tsakiya […]
Tsohon Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya kara kwankwantsa Sanata Basheer Garba Lado da kasa, bayan da Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta Jihar Kano, ta yi watsi da karar da ya kai gabanta yana kalubalanta nasarar Kwankwaso a zaben da ya gabata.
Sanata Bashir Garba Lado wanda ya tsaya takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a Jam’iyyar PDP a zaben watan Maris ya bukaci kotun ne ta soki nasarar Kwankwaso bisa hujjar cewa an sauya sunan Alhaji Abba Kabir Yusuf ne da sunan wanda yake kara kuma hakan bai dace ba. Ya ce
Alkalin kotun Mai shari’a Corneleaus Akintayo ya yi watsi da karar bisa rashin hujjar gabatar da ita tunda farko, inda ya kara da cewa mai karar ya gaza tabbatar da hujjar zargin da yake yi. Ya ce Lado ya gaza gabatar da wata shaida da za ta sa a rushe zaben wanda yake kara don haka ya kori karar.
Ya ce bukatar mai kara na kotun ta soke zaben saboda an canja sunanAlhaji Abba Kabir Yusuf da na wanda yake kara ba zai samu ba. Ya ce kotun ba ta ga wata hujja da za ta soke ko ta haramta zaben ba, don haka ta amince da cewa zaben ya inganta.
Mai shari’a Akintayo ya ce mai kara ya gaza bayar da ingantacciyar shaida da za ta nuna cewa sakamakon zaben bai dace da yadda aka gudanar da zaben ba.
Yanke hukuncin ke da wuya sai magoya bayan tsohon Gwamnan da suka tattaru suna jiran sakamakon hukuncin a harabar kotun suka barke da sowa da shagulgula.