Sarautar Kano: Babu barazanar da wani zai yi mana —Kwankwaso

“…Ba za mu lamunci barazanar siyasa ba, domin mu kwararrun ’yan siyasa ne kuma mun san duk hanyoyin magance kowane irin shedanci” in ji Kwankwaso

Sarautar Kano: Babu barazanar da wani zai yi mana —Kwankwaso

Dan takarar shugaban kasan Jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi Gwamnatin Tarayya da biye was shawarar makiyan Kano don wargaza zaman lafiya da aka san jihar.

Da yake tsokaci kan rikicin Sarautar Kano, Kwankwaso ya ya zargi hukumomin tsaron Gwamnatin Tarayya da goyon baya Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, sabanin aikinsu na tabbatar da tsaro da kuma doka da oda a jihar.

A cewarsa, “Muna da dimbin mabiya saboda jama’a sun amince da mu kasancewar muna tare da su, kuma a shirye gwamnain NNPP take ta yi wa duk wadanda suka zabe ta aiki.”

Tsohon gwamnan Kano ya ci gaba da cewa, a matsayin ’yan siyasa, “Ba za mu nade hannu mu zura ido mu bar makiyan Kano su wargaza zaman lafiyan da aka san jiharmu ba.”

Don haka ya lashi takobin yin fito-no-fito da duk wani yunkuri yin zagon kasa ga gwamnati da mahukuntan Jihar Kano.

Kwankwaso ya yi wannana jawabi ne a lokacin taron bikin kaddamar da aikin titi mai nisan kilomita 82 a mahaifarsa, Karamar Hukumar Madobi da gwamnatin jihar za ta gina.

A cewarsa, “Za mu yi duk mai yiwuwa wajen goyon bayan gwamna da ganin ya yi nasara.

“Na ji dadi da ganin wani abu bai dauke hankalinsa ba, ya mayar da hankali wajen cimma manufar da aka sa gaba.

“Akwai wasu Kanawa makiyan wannan jihar da ke fama da tabin hankali, da ke ba wa Gwamnatin Tarayya shawara cewa ta kwace ikon Kano ta hanyar kafa dokar ta-baci.

“Wannan kololuwar rashin hankali ne, kuma al’ummmar Kano a shirye suke su yaki wannan shirmen,” in ji Kwankwaso.

A cewarsa, “Ganin cewa zaben 2027 na tafe, wasu rudaddun ’yan siyasa sun fara shirin kawo mana yamutsi, to su sani cewa ba za mu zura musu ido ba, gara a fasa kowannenmu ya rasa da mu kyale su su muttsike mu babu gaira babu dalili.

“Muna kalubalantar duk wanda ke ganin zai iya mana zagon kasa a siyasance ga fili ga mai doki, ya sani cewa a shirye muke mu gwabza da shi.

“Ba ma tsoron rasa mulki domin ko babu mulki za mu ci gaba da zama ’yan siyasa, kuma ba za mu guje wa kaddarar mu ba. Mu ’yan Adam ne kuma mun san abin da zai amfane mu, don haka za mu ci gaba da nemansa wurjanjan,” in ji tsohon gwamnan.

Jagoran NNPP ya zargi Gwamnatin da biye wa wasu Kanawa marasa kishi wadanda ba za su amfane ta da komai ba, sai su jawo mata faduwa zabe domin al’ummar Kano ba za su lamunci duk wani zagon kasa ga gwamnatin jihar ba.

“A shirye muka a yi sulhu, amma ba za mu lamunci kowane irin barazanar siyasa ba. Mu kwararrun ’yan siyasa ne kuma mun san duk hanyoyin da za mu yi maganin kowane irin shedanci,” in ji Kwankwaso.