Kwankwaso ya shawarci masu shirin zanga-zanga

Na fahimci damuwarku da kuma burin kawo sauyi, amma za ku iya sauya shugaba da

Kwankwaso ya shawarci masu shirin zanga-zanga

Kwankwaso

Madugun jam’iyyar NNPP a Nijeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shawarci matasan da ke shirin soma zanga zangar matsin rayuwa a faɗin ƙasar.

Cikin wani dogon sako da tsohon gwamnan na Kano ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya shawarci masu shirin gudanar da zangar-zangar da su yi dogon nazari kafin aiwatar da abin da daga baya za su yi da na sani.

Kwankwaso ya bayyana cewa ’yan Najeriya sun tsinci kansu a ƙuncin rayuwa saboda kuskuren shugabanni tun 2007 amma duk da haka ya ce akwai damar gyara.

“Abin takaici ne yadda ɗabi’un shugabanninmu na rashin jagoranci nagari ya jefa ‘yan ƙasa musamman matasa cikin fushi da yunwa da rashin tsaro da ɗeɓe tsammanin kan samun wani tudun dafawa a ƙasar.

“Kurakuran da Gwamnatin Tarayya ta tafka kan dambarwar Masarautun Kano da tsige Mataimakin Gwamnan Edo da rikicin siyasa a Jihar Ribas da yi wa Matatar Mai ta Dangote zagon ƙasa da cece-kucen da ta haddasa kan yarjejeniyar SAMOA da rikicin Sanata Ali Ndume da shugabancin jam’iyyar APC baya ga rashin tsaro da ke ci gaba yaduwa da sauran miyagun ayyuka, duk wasu ‘yan misalai ne na rikice-rikicen da tana iya kawar da su.

“Saboda haka muna kira ga shugabanni a kowane mataki da su ɗauki matakan da suka dace domin magance wannan ɗimbin ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta.”

Ya ce zanga-zangar da matasa ke shirin yi ta ƙara nuna ɓacin ran da mutane ke ciki da kai su bango saboda halin da suka shiga la’akari da wadannan kurakurai da gwamnati ta gaza magancewa.

Kwankwaso wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP a Zaben 2023 ya roƙi ’yan Nijeriya da su zama masu kishin ƙasa sannan su ƙara hakuri wajen bai wa gwamnati goyon baya domin ta samu nasara.

Ya  bayyana cewa maimakon wannan zanga-zanga matasa na da damar canza duk shugaban da ya gaza ta hanyar kuri’unsu a lokacin zaɓe.

Kwankwaso ya kuma yi gargaɗin cewa zanga-zanga na iya rikidewa ta zama tarzomar da ka iya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

“Na fahimci damuwarku da kuma burin kawo sauyi, duk da haka ina roƙon ku duba sakamakon da ka iya biyo bayan zanga-zangar.

“A maimakon haka ku bi hanyar da ta dace wajen kawo canji, ku yi amfani da karfin kuri’unku,” a cewar Kwankwaso.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos