Kwankwaso ya shirya wa ’yan fim shan ruwa

A ranar Lahadi ne Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabi’u Kwankwaso ya shirya wa ’yan fim shan ruwa a gidan gwamnatin jihar.Shugaban kungiyar ’yan fim na Arewa Film Makers Association of Nigeria (AFMAN) reshen Jihar Kano, Isma’il NaAbba Afakallah ne ya jagoranci ’yan fim zuwa shan ruwa da gwamnan.A yayin da Kwankwaso ke jawabi ne, ya […]

Kwankwaso ya shirya wa ’yan fim shan ruwa
Kwankwaso ya shirya wa ’yan fim shan ruwa

A ranar Lahadi ne Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabi’u Kwankwaso ya shirya wa ’yan fim shan ruwa a gidan gwamnatin jihar.
Shugaban kungiyar ’yan fim na Arewa Film Makers Association of Nigeria (AFMAN) reshen Jihar Kano, Isma’il NaAbba Afakallah ne ya jagoranci ’yan fim zuwa shan ruwa da gwamnan.
A yayin da Kwankwaso ke jawabi ne, ya yaba wa ’yan fim bisa gudunmuwar da suke bayarwa wajen samar da ayyukan yi.
Ya ce: “Aikin yi ko Amurka yana da wuya, don haka abin a yaba wa ’yan fim ne sakamakon ayyukan da suke samarwa. Don taimaka wa harkar fim ne ya sa Gwamnatin Jihar Kano ta samar da makarantar koyon aikin fim da kuma wuraren daukar fim.”
Gwamnan ya ba ’yan fim shawara kan su ci gaba da yin fina-finan da suka yi daidai da al’ada da kuma addini.
Da yake a kurarren lokaci ’yan fim suka isa gidan gwamnatin, ya sanya babu wani dan fim da ya yi jawabi face jawabin godiya da jagoran ’yan fim Afakallah ya yi ga gwamnan.
A cikin ’yan fim din da suka halarci shan ruwan akwai Ali Nuhu da Hamisu Iyan-tama da Ibrahim Mandawari da Fati Baffa da sauransu.