Kwankwaso ya yi Allah-wadai da ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas

Kwankwaso ya yi Allah-wadai da yadda Majalisar Dokoki suka zama ‘yan amshin-shata.

Kwankwaso ya yi Allah-wadai da ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas.

Kwankwaso ya ce matakin da Tinubu ya ɗauka ya saɓa doka kuma barazana ne ga dimokuraɗiyya.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Kwankwaso ya gargaɗi cewa irin wannan matakin na iya kafa mummunan misali da kuma illata dimokuraɗiyya a Najeriya.

Kwankwaso, ya ruwaito yadda rikicin siyasa da ya haifar da soke zaɓen 1993, inda ya jaddada cewa ‘yan majalisa su daina ɓata lokacinsu kan abubuwan da ba su dace ba.

“Majalisa tana da alhakin sa ido kan ayyukan ɓangaren zartarwa, ba wai kawai yarda da duk abin da ta ce ba.

“Abu ne mai matuƙar tayar da hankali ganin yadda Majalisar Tarayya ta 10 ta fi kowace zama ‘yar amshin shata ga ɓangaren zartarwa,” in ji shi.

Tsohon gwamnan ya kuma soki yadda Majalisar Tarayya ta gaggauta amincewa da matakin Shugaba Tinubu ba tare da bin ƙa’idojin da kundin tsarin mulki ya tanada ba.

“Kundin tsarin mulki ya fayyace yadda ake yanke hukunci kan irin wannan matsala, amma ‘yan majalisa sun zaɓi amfani da murya wajen zaɓe, wanda hakan yana janyo shakku kan sahihancin lamarin.

“Gaggawar amincewa da dokar ta-ɓaci da zata kifar da gwamnatin da aka zaɓa, cin fuska ne ga dimokuraɗiyya,” in ji shi.

Kwankwaso ya kuma yi gargaɗi kan shigar sojoji cikin harkokin mulki, inda ya bayyana cewa hakan tamkar komawa baya ne bayan ci gaban da aka samu tsawon shekaru 26 na dimokuraɗiyya.

Ya bayyana damuwarsa cewa wannan matakin na iya zama wata dabara ta murƙushe jihohin da ba sa tare da jam’iyya mai mulki.

“A matsayinsa na wanda ke da’awar kare dimokuraɗiyya, Shugaba Tinubu ya kamata ya fi kowa fahimta cewa kawo sojoji cikin mulki hatsari ne.

“Wannan matakin ba wai kawai barazana ne ga zaman lafiya ba, yana iya zama hanyar kama-karya idan ba a dakatar da shi ba,” in ji Kwankwaso.