Kwankwaso ya zargi EFCC da zama karyar farautar siyasa
Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce siyasa ce ta sa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) ta kama wasu jami’an Majalisar Dokokin Jihar. Gwamna Rabi’u Kwankwaso ya ce kama manyan jami’an majalisar da EFCC ta yi abin takaici ne kuma koma baya ga dimokuradiyyar kasar nan.Ya ce an […]
Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce siyasa ce ta sa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) ta kama wasu jami’an Majalisar Dokokin Jihar. Gwamna Rabi’u Kwankwaso ya ce kama manyan jami’an majalisar da EFCC ta yi abin takaici ne kuma koma baya ga dimokuradiyyar kasar nan.
Ya ce an kama jami’an ne domin cin mutuncinsu sakamakon komawarsu jam’iyyar adawa ta APC daga Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar nan.
Sai dai Hukumar EFCC ta musanta wannan zargi na Gwamna Kwankwaso, inda ta ce ta gayyaci jami’an majalisar ne zuwa Abuja, babban birnin tarayya, bayan da wani babban mutum a Kano ya zargi ’yan majalisar da saba wa dokar kasafin kudi.
Hukumar ta EFCC ta yi awon gaba da shugabanni da manyan ma’aikatan majalisar jihar Kano ne a ranar Litinin da ta gabata da sunan binciken gyaran kasafin kudin jihar na bana.
Shugaban kwamitin bin diddigin yadda ake kashe kudin gwamnati na majalisar Alhaji Rabi’u Sale Gwarzo wanda ba ya cikin wadannda aka gayyata, ya shaida wa gidan rediyon BBC cewa shugabannin majalisar takwas da kuma ma’aikata uku aka gayyata.
A cewar Rabi’u Gwarzo takardar gayyatar da EFCC ta aike wa majalisar ta ce gayyatar tana da dangantaka da gyaran kasafin kudin da gwamnatin jihar ta nemi ’yan majalisar su yi a makon jiya ne na Naira biliyan 28.
Sai dai manazarta na ganin hakan ba zai rasa nasaba da siyasa ba, musamman ma da Gwamnan Jihar Injiniya Rabi’u Kwankwaso ya koma Jam’iyyar APC.
Sai dai an ba da belin Shugaban Majalisar Alhaji Gambo Sallau da sauran shugabannin majalisar 11 a ranar Talatar da ta gabata, inda ya jagoranci zaman majalisar lokacin da Gwamna Kwankwaso ya gabatar da kasafin jihar na shekarar da zamu shiga.
Gwamna Kwankwaso wanda da kansa ya tarbi ’yan majalisar a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano kafin su zarce majalisar don gabatar da kasafin Naira biliyan 219 da miliyan 281 ya ce wasu mutane ne bisa umarni daga sama suka kame shugabannin majalisar ba bisa doka ba. Ya ce “babu wanda zai iya musguna wa wakilan Jihar Kano. Kuma wannan wani yunkuri ne da ka iya jawo rikici da wargaza zaman lafiyar da jihar ta samu. Don haka ina kira ku dauki wannan musgunawa a matsayin taku sadaukarwa ga jihar.” Daga nan sai ya gabatar da kasafin na badi tare da bayyana cewa kasafin bana ya samu gagarumar nasara ta aiwatar da kashi 62 cikin 100.