Kwanon kuturu

Wasu matasa ne suka yi Maulidi, da gari ya waye aka hado shayi don karyawa. A cikinsu akwai wanda ya kwana da yunwa, kafin ya ankara kofuna sun kare. Yana lellekawa sai ya hango wani kwano, ya dauko ya diba. Ya soma sha ke nan sai ya ga wani kuturu a tsaye kusa da shi. […]

Kwanon kuturu
Kwanon kuturu

Wasu matasa ne suka yi Maulidi, da gari ya waye aka hado shayi don karyawa. A cikinsu akwai wanda ya kwana da yunwa, kafin ya ankara kofuna sun kare. Yana lellekawa sai ya hango wani kwano, ya dauko ya diba. Ya soma sha ke nan sai ya ga wani kuturu a tsaye kusa da shi. Ya dubi kuturun cikin kyama ya ce: “Malam, a ci gaba!” Kuturu da ya fusata sai ya ce: “Kai, don Allah ja can, ni ba shayinka nake jira ba; kwanona nake jira ka sha ka ba ni.”

Daga Sulaiman Gombe