Kwapchi Bata Dibal: Rayuwa a matsayin mai gabatarwa a gidan talabijin

Kwapchi Bata Dibal fitacciyar ’yar jarida ce, kuma ita ce mai ba Gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima shawara kan harkokin watsa labarai. Ta yi bayanin matsaloli da kuma alfanun rayuwarta a matsayin mai gabatarwa a gidan talabijin. Sunana Kwapchi Bata Dibal, an haife ni a ranar 29 ga Maris, 1980. Sunan mahaifina Bata Dibal, sunan […]

Kwapchi Bata Dibal: Rayuwa a matsayin mai gabatarwa a gidan talabijin

Kwapchi Bata Dibal fitacciyar ’yar jarida ce, kuma ita ce mai ba Gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima shawara kan harkokin watsa labarai. Ta yi bayanin matsaloli da kuma alfanun rayuwarta a matsayin mai gabatarwa a gidan talabijin.

Sunana Kwapchi Bata Dibal, an haife ni a ranar 29 ga Maris, 1980. Sunan mahaifina Bata Dibal, sunan mahaifiyata Misis Mwajim Bata. Mahaifana masana ne a harkar ilimi, dukkansu ’yan kauyen Durkwa da ke karamar Hukumar Hawul a Jihar Barno ne. Na fara karatun firamare a Shehu Garbai Primary School da ke Maiduguri, na kammala Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Mungono a shekarar 1998, daga nan na karanta aikin jarida a Jami’ar Maiduguri. Na kammala jami’a a shekarar 2004. Na kammala hidimar kasa a Jihar Abiya a shekarar 2006.  Daga nan na fara aiki a gidan talabijin na Najeriya (NTA) a Maiduguri. Bayan nan wata cibiya mai suna bolkswagen Foundation da ke kasar Jamus ta dauki nauyin karatuna kashi biyu a jami’ar Unibersity of Music Hanober da ke Jamus da kuma jami’ar Unibersities of Legon and Cape Coast da ke kasar Ghana. Gwamnatin Jihar Barno ta dauki nauyina har na yi kwasa-kwasai biyu a shekarar 2011 da kuma 2012 a makarantar kwarewa a aikin jarida da ke Landan mai suna London School of Journalism. A yanzu ni ce mai ba Gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima shawara kan harkokin watsa labarai.
Yadda na taso a cikin gidanmu
Ni ce ta shida cikin mu 7 a wurin mahaifanmu. Na farko ya rasu. Don haka na taso a cikin yayuna ne, ina da yayu mata da kuma maza, wadanda suke sa ido kan yadda nake gudanar da rayuwata, ina da kanwa daya. Makaratun da na yi da kuma abokan da na hadu da su da yadda na taso a tsakanin yayuna ya ba ni damar sanin makamar yadda zan yi mu’amala da mutane. Ina da kusaci da mahaifana. Mahaifina ya sanya mini sunan mahaifiyarsa ne, don haka ya mayar da ni shalelensa, ba ya ganin laifina, mahaifana sun yi ayyuka a wurare da garuruwa daban-daban. Don haka dukkansu kowa yana tafiya wurin aikinsa, duk da haka muna tare da su duk ranakun karshen mako. A ranakun karshen mako mukan je mu yi sayayya, sannan mu yi ziyarci wurare daban-daban. Mahaifiyata shugabar makarantar sakandare ce, don haka an rika canza mata makarantu.
Abubuwan da ba zan manta da su ina karama ba
Ina tuna yadda babban yayanmu idan ya dawo daga makaranta muke taryarsa, mukan yi tafiye-tafiye tare, mu ci abinci tare, mu yi addu’a tare, har yanzu akwai shakuwa a tsakaninmu. Mahaifiyarmu (marigayiya) ta yi kokarin wajen hada kanmu, kuma har yanzu kanmu a hade yake. Muna taimaka wa juna. Ta ba mu kwarin gwiwar jajircewa a kan duk wani abu da muka sa a gaba, ta ce mu rika sanya Allah a dukkan al’amuranmu za mu samu nasara. Wannan ya sanya muka samu nasara a dukkan bangarorin da muke kai yanzu haka. Nakan tuna yadda muke guna-guni duk lokacin da za ta dawo gida don yin hutun karshen mako, muna guna-guni ne domin za ta ce mu wanke tufafinmu, sannan mu yi girki, idan ba ta nan ba ma aiki domin mahaifinmu ya riga ya dauka mana ’yan aiki, amma sai ta ce dole sai mun yi, idan ba haka ba ta yaya za mu koya, zan iya tunawa tun ina aji 4 na firamare nake iya dafa abinci, amma da taimakon ‘malama’, sunan da muke kira mahaifiyarmu ke nan. Nakan iya tuna lokacin da muke rawa a gaban mahaifanmu dauke da sakamakon jarrabawa, saboda mun yi abin kirki, inda suke ba mu kyaututtuka. Mahaifanmu suna da hanyoyin da suke hana mu fita yawo don kada mu yi abota da gurbatattun abokai. Mahaifanmu ne suke tantance mana abokai.
Rayuwa a matsayin mai gabatarwa a gidan talabjin
Babu kalubale sosai a matsayina ta mai gabatarwa a gidan talabijin kamar a ce ina aiko da rahoto. A bangaren aikin jarida ina kallon gabatarwa kamar aiki malalata, mai gabatarwa zai sanya tufafi mai kyawu sannan ya rika gabatar da rahotannin wakilai daban-daban, wadanda suka sha wahala kafin su hada labarinsu. Aikin gabatarwa ma na bukatar fikira da fasaha da kuma kirkirar salon gabatarwa, za iya rahoto mai kyawu amma wajen gabatarwa a bata shi, idan kana matsayin mai gabatarwa za ka karanta rahoto ko kuma wanda ya yi rahoton ya fada mini yadda rahoton yake kafin a gabatar da shi, don haka hanya ta farko da za ka zama dan jarida mai kyawu ita ce, samun labari da kuma bayar da shi yadda ya dace. Rayuwa a matsayin mai gabatarwa ta ba ni farin jini a wurin mutane, sannan tana da hadari, saboda kowa ya san ka, kai kuma ba ka san kowa ba. Ba zan manta ba, wani yaro mai suna Joshua dan shekara 14 ya kira ni yana kuka daga Mubi, ya ce mini ya kasance masoyina, don haka ya samu labarin mahaifiyata ta rasu, hakan ya sa aka nema masa lambata, wanda ga shi ya kira ni don ya yi mini ta’aziyya.

Yadda na ji ranar da na fara gabatarwa
Na dade da ina da burin a dora mini kyamara, don haka bayan na fara aiki da NTA a shekarar 2006 sai na kara kwantar da hankalina, na ce wata rana za dora mini kyamara, kodayake na fara a matsayin wakiliya ce, a lokacin ni ce karama a dakin watsa labarai, don haka ba na tsammanin zan fara gabatarwa, saboda akwai wadanda suka dade a aikin, wata rana wani mai gabatarwa bai samu damar zuwa ba, da ma kuma kullum ba ya zuwa wurin aiki da wuri, a lokacin ina da labarin da na hada, sannan ’yan mintuna suka rage 7 na dare ta cika. Na hada kayana zan tafi gida ke nan, sai furodusa ya ce babu mai gabatarwa ko daya, don haka zan zama mai gabatarwa, ban san lokacin da na rika gumi a dakin watsa labarai bayan ya fada mini ba, duk da cewa akwai na’urar AC, cikin sauri na yi bitar labaran da za a gabatar ba tare da an yi mini kwalliya ba saboda lokaci ya kure. Na karanta kanun labaran da kyau, amma bayan na kalli gefe ne, na gan ni a cikin talabijin, sai na ce yanzu kowa yana kallo na, a lokacin na tsorata kamar in gudu, sai na yi ta ’yan maza. Daga nan na ci gaba, duk da na yi kura-kurai, amma da yawa sun ce na yi kokari sosai, musamman ma da suka ji an sanya in yi labaran a kurarren lokaci ne. Daga ranar aka sanya sunana a rijistar masu gabatarwa da kuma karanta labarai.
Burina ina karama
Tun ina karama nake da burin zama ’yar jarida, duk da cewa a lokacin ban san yaya aikin yake ba. A lokacin da nake firamare nakan kalli marigayi Yinka Craig a NTA, hakan ya sa nake sonsa. Wata rana sai na fada wa kaina cewa ni ma wata rana zan girma in rika karanta labarai a gidan talabijin kamarsa, sannan zan aure shi. Zan iya tuna lokacin da mahaifiyata take shugabar makarantar sakandaren ’yan mata da ke Nguru, inda wata rana na same ta, na ce mata ina so in zama kamar dan jarida marigayi Yinka, sai ta ce mini ya zama dole in iya magana da kuma rubuta Turanci da kyau, wannan dalilin ya sa na mayar da hankali wajen darussan Turanci, da taimakonta na fahimci yaya aikin jarida yake.
Mutanen da nake koyi da su
Mutanen da nake koyi da su sun hada da marigayi Yinka Craig da mahaifiyata da Nelson Mandela da Shugabar kasar Laberiya Sirleaf Johnson da Christiana Amanpour da kuma mai gabatarwa Elizabeth Banu.