Kwararar ’yan gudun hijira ta haifar da tsadar gidajen haya a Maiduguri

Kwararar ’yan gudun hijira zuwa garin Maiduguri ya jawo tsadar kudin gidajen haya a birnin, sakamakon yadda akasarin rukunin gidaje masu saukin kudin da gwamnatin Jihar Borno ta gina da kuma wasu makarantu suka koma sansanonin ’yan gudun hijirar. Akasarin sansanonin da gwamnatin ta tanada da suka kai 10, sun cika suka batse har wasu […]

Kwararar ’yan gudun hijira ta haifar da tsadar gidajen haya a Maiduguri
Kwararar ’yan gudun hijira ta haifar da tsadar gidajen haya a Maiduguri

Kwararar ’yan gudun hijira zuwa garin Maiduguri ya jawo tsadar kudin gidajen haya a birnin, sakamakon yadda akasarin rukunin gidaje masu saukin kudin da gwamnatin Jihar Borno ta gina da kuma wasu makarantu suka koma sansanonin ’yan gudun hijirar.

Akasarin sansanonin da gwamnatin ta tanada da suka kai 10, sun cika suka batse har wasu na fita daga sansanonin zuwa gidajen ’yan uwansu ko na haya, lamarin da ya sa a yanzu haka samun gidan haya ya zama wahala ga ’yan gudun hijirar.
Malam Muhammadu Mainono Baga, na daya daga cikin ’yan gudun hijirar da suke neman gidan haya a Maiduguri, kuma ya shaida wa Aminiya cewa: ‘‘A gaskiya ba zan iya zama a sansanin ’yan gudun hijira ba, shi ne na fito neman gidan haya amma sai na tarar da tsada ainun ba zan iya biya ba, kodayake na samu na kubuto da iyalina, amma ina bukatar wuri mai sauki ne ta yadda rayuwata da iyalina za ta gudana cikin sauki.”
Ya yi kira gara ga masu gidajen haya su yi sauki da rangwame saboda su ’yan gudun hijirar suna cikin tsanani, ganin sun bar garuruwansu ba da son ransu ba.
Binciken Aminiya ya gano ana karbar Naira dubu biyu kowane wata kan kowane daki irin na masu karamin karfi kuma dole sai mutum ya lale na shekara daya akalla wato Naira dubu 24, kudin da galibin ’yan gudun hijirar suka ce ba su da su. Wasu daga cikin ’yan gudun hijirar dai ala tilas suka koma sansanin ’yan gudun hijirar saboda ba za su iya biyan kudin hayar ba.
daya daga cikin dillalan gidajen hayar mai suna Hassan Aliyu, ya ce ba laifinsu ba ne, hauhawar farashin kayan gini ne kamar siminti da yashi da sauransu suka sa masu gidaje suke tsawwala kudin hayar, “Mu dai sukan ce mana ga abin da suke so kuma babu abin da za mu iya yi,” inji shi.