Kwararru da masu masan’antu sun ce akwai yiwuwar sake shiga matsin tattalin arziki a badi

Wasdanu masana tattalin arziki da kuma masu masana’antu sun ce, gargadin da Kungiyar Gwamnoni ta Najeriya ta yi kan yiyuwar sake fuskantar matsin tattalin arziki, a badi  yana da alamar kanshin gaskiya. Gwamna Abdul’aziz Yari na Jihar Zamfara, kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya ne ya yi gargadin inda  ya ce ’yan Najeriya su shirya wa […]

Kwararru da masu masan’antu sun ce akwai yiwuwar sake shiga matsin tattalin arziki a badi

Manyann baqi a wurin taron nusar da sababbin zabavvun gwamnoni da wadanda suka koma karo na biyu

Wasdanu masana tattalin arziki da kuma masu masana’antu sun ce, gargadin da Kungiyar Gwamnoni ta Najeriya ta yi kan yiyuwar sake fuskantar matsin tattalin arziki, a badi  yana da alamar kanshin gaskiya.

Gwamna Abdul’aziz Yari na Jihar Zamfara, kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya ne ya yi gargadin inda  ya ce ’yan Najeriya su shirya wa kalubalen tattalin arzikin da za a sake fuskanta, a badi.

Gwamnan ya yi gargadin ne, a wani taron bita da Sakataren Gwamnatin Tarayya ya shirya wa sababbin gwamnonin da aka zaba da masu zarcewa a mulki a Abuja, a farkon nan.

Ya fada wa gwamnonin cewa, tafiyar ba za ta kasance mai sauki ba, yana mai cewa gwamnoni masu barin gado, sun yi kokari sosai ta fuskar samar da ababen more rayuwa da sauran ababuwan ci gaban jama’a, sakamakon yadda suka samu farashin man fetur ya fadi daga Dalar Amurka 100 zuwa 114, kan kowacce ganga da aka rika samu daga shekarun 2011 zuwa 2014.

A cewar Yari a shekarar 2014, farashin danyen man wanda shi ne kusan kacokan abin da gwamnati ta dogara wajen samun kudaden shiga, ya yi kasa zuwa Dala 75 a kan kowace ganga, wanda hakan ya janyo jihohi da dama ke faman yadda za su ma’aikata albashi.

A cewarsa: “Wannan batu ankararwa ne gare ku baki daya (gwamnoni) ku shirya wa fuskantar kalubalen matsin tattalin arziki, musamman ganin akwai yiyuwar sake tsunduma cikin wani sabon matsin tattalin arziki a shekara mai zuwa, wanda kuma zai iya zama har rubu’in shekarar 2021. Amma kwarewarku wajen ririta arziki, zai taimake ku cikin irin wannan hali, idan ma har ya faru.” Ya bukaci gwamnonin su bunkasa tattalin arzikin jihohin, yadda zai yi daidai da zamani.

Ya ce, dole ne Najeriya ta kara duba bukatar fadada hanyoyin kudaden shiga ta fuskar saka jari a harkokin hakar ma’adinai da noma da sauran albarkatu, don fitar da kasar nan daga kangin fadawa cikin matsin tattalin arziki, wanda yawan dogaro da man fetur yak e haifarwa.