Kwararru sun yi hasashen tattalin arziki zai yi kyau bana
Kwararru daban-daban sun yi hasashen samun bunkasar tattalin arzikin Najeriya a shekarar 2018. Wani kwararre kan harkokin kudi kuma shugaban sashen ilimin bankuna da kudi a jami’ar Nasarawa da ke Keffi, Dokta Uche Uwaleke ya ce akwai yiwuwar samun ci gaba a tattalin arzikin Najeriya idan aka yi la’akari da shika-shikan da ke tallafawa […]
Kwararru daban-daban sun yi hasashen samun bunkasar tattalin arzikin Najeriya a shekarar 2018.
Wani kwararre kan harkokin kudi kuma shugaban sashen ilimin bankuna da kudi a jami’ar Nasarawa da ke Keffi, Dokta Uche Uwaleke ya ce akwai yiwuwar samun ci gaba a tattalin arzikin Najeriya idan aka yi la’akari da shika-shikan da ke tallafawa arzikin kasar musamman ta bangaren kudin shigar da kasar ke samu daga bangaren mai.
Uwaleke ya yi hasashen cewa ta yiwu babban bankin Najeriya na CBN zai ci gaba da bin dokokin tsarin kudi na zangon farko na shekarar nan.