kwararrun malamai da kayan aiki makarantarmu ke bukata – Yahaya Wanzam
Makarantar koyon sana’a mai zaman kanta ta Kazaure a Jihar Jigawa za ta ci gaba da horar da matasa, don zama masu dogaro da kai a cikin al’umma, amma a cewar Shugaban Maakranta, Malam Yahaya Wanzam kudurin makarantar zai tabbata ne idan masu hannu da shuni da hukuma suka hada karfi wajen taimaka wa matasan […]
Makarantar koyon sana’a mai zaman kanta ta Kazaure a Jihar Jigawa za ta ci gaba da horar da matasa, don zama masu dogaro da kai a cikin al’umma, amma a cewar Shugaban Maakranta, Malam Yahaya Wanzam kudurin makarantar zai tabbata ne idan masu hannu da shuni da hukuma suka hada karfi wajen taimaka wa matasan da kayan aiki da kwararrun malamai.
daya daga cikin masu kishin taimaka wa matasa a jihar, Malam Yahaya Abdullahi Kazaure, ya dauki matasa maza da mata mutum 80, wadanda yake koya wa sana’ar dinki da masu koyan sabulun wanka da man shafawa, a wata makaranta da ke kauyen Karaftayi, a yankin karamar Hukumar Kazaure. Yawancin wadanda ke koyon sana’ar yara ne da shekarunsu ya kama daga 15 zuwa 20; suna kokarin zuwa makaranta.
Malam Yahaya, wanda shi ne shugaban makarantar, a hirar da ya yi da Aminiya, ya jero matsalolin da ke kawo wa makarantar tarnaki wajen gudanar da ayyukanta, wadanda suka ahda da karancin malamai masu koyar da sana’o’i da rashin kayan aiki, inda ya ce wadannan matsaloli sun yi kamari har ta kai ga malamai ba sa iya koyar da abubuwan da suka kamata a ce sun koya wa matasan. Don haka ya bukaci hukumomin jihar da na kananan hukumomi da masu hannu da shuni da ke fadin jihar da su taimaka wajen inganta harkokin karatu a makarantar.
“kwazon Gwamnatin Jihar Jigawa wajen samar wa matasa ayyukan yi ke zaburar da masu kishin kasa da kamfanoni, su tallafa wajen hana zaman kashe wando a tsakanin al’ummar jihar. Don haka muke himmatu wajen bai wa matasa horo. Muna kuma fatan gweamnati da masu hannu da shuni za su shigo mu hada karfi don cimma manufa guda,” inji shi.
Ya ce, akwai bukatar a samar da isassun kekunan dinki da kayan aikin koyarwa, wadanda suka hada da sinadaran yin sabulu. “Don ta haka ne kawai malamai za su ji dadin koyarwa. Matasa maza da mata da sun kamala samun horo su ji dadin tsayuwa da kafarsu,” a cewarsa
Wata daliba dake koyan dinki a makarantar, Malam Zuwaira Sani Karafayi, ta tofa albarkacin bakinta, da cewa sun sami karuwa matuka wajen koyan sana’ar domin yanzu haka ta koyi yanka da dinkin mata, abin da ya rage mata ta mallaki kekenta da za ta fara sana’a don dogaro da kanta, musamman idan Allah ya kawo mata miji tayi aure.
Shugaban makarantar ya karkare bayanansa, inda ya bukaci Hukumar Samar da Aikin yi ta kasa, wato “NDE” da ta sanya makarantar a cikin shirye-shiryenta, ta yadda duk wanda ya kamala samun horo za a tallafa masa da kayan aiki ko jarin yin sana’a. “A samar mana da malamai da isassun kayan aiki, don cimma manufar gwamnati ta hana zaman banza da kashe wando a tsakanin matasa,” inji shi.