kwarorin da ake zargi da tara makamai a Kano sun sake gurfana a kotu
kwarori uku ’yan Najeriya da aka kama bisa zargin hannunsu a ayyukan ta’addanci a kasar sun sake gurfana a gaban wata Babbar Kotun Abuja a shekaranjiya Laraba.kwarorin Mustapha Fawaz da Abdallah Tahini da Talal Ahmad Roda, mamallaka kantin Amigo Supermarket da lambun shakatawa na Wonderland Amusement Park da ke Abuja, an gabatar da su gabann […]

kwarori uku ’yan Najeriya da aka kama bisa zargin hannunsu a ayyukan ta’addanci a kasar sun sake gurfana a gaban wata Babbar Kotun Abuja a shekaranjiya Laraba.
kwarorin Mustapha Fawaz da Abdallah Tahini da Talal Ahmad Roda, mamallaka kantin Amigo Supermarket da lambun shakatawa na Wonderland Amusement Park da ke Abuja, an gabatar da su gabann kotun ne kan tuhume-tuhume shida da suke da alaka da ta’addanci. Sai dai dukkansu sun musanta tuhume-tuhumen.
An gabatar da su gaban kotun ne tare da Amigo Supermarket da kuma Wonderland Amusement Park.
Da farko an gurfanar da mutanen ne a gaban wata Kotun Majistare da ke Karu, amma sai Hukumar Tsaron kasa (SSS) ta janyye tuhumce-tuhumcen da ake yi musu inda tta kafa hujja da rashin hurumi ga kotun.
Sababbin tuhumce-tuhumcen da Gwamnatin Tarayya ke musu, sun hada da kasancewarsu ’ya’yan bangaren soja na kungiyar Hezbollah kuma ana zargin sun samu horo kan yadda za su iya aikata ayyukan ta’addanci.
Har wa yau ana tuhumarsu da karbar kudin ’yan ta’adda da kuma boye wa hukumomin tsaro bayanan da za su taimaka musu wajen kama wani mutum da ke da hannu a ayyukan ta’addanci.
Kowane daya daga cikin tuhumce-tuhumcen ana iya daurin shekara 10 a kansa.
Lauyansu, Ahmed Raji (SAN), ya roki kotun kan a ci gaba da tsare wadanda yake karewa a hannun Hukumar SSS bisa hujjar cewa gidan kurkuku ba ya da wadatattun kayan da za a iya tsare su, matsayin da mai gabatar da kara ya goyyi bayansa.
Tun farko wata wasika da Kwanturolan Gidajen Yari ya rubuta game da wani batu na ta’addanci ta bayyana cewa ba ya da wurin da zai iya tsare irin wadannan manyan ’yan ta’adda da ake zargi.
Wadanda ake tuhumar sun gabatar da wata takarda suna kalubalantar hurumin kotun na sauraren wannan shari’a. Kuma sun nemi a bayar da belinsu tare da bude wuraren gudanar da harkokin kasuwancinsu.
Daraktan Gabatar da kararraki, Simon Egede ya nemi kotun ta ba shi lokaci domin ya mayar da martani kan wannan bukata.
Lokacin da yake dage zaman shari’ar zuwa 8 ga Yuli don fara saurarar bukatar, alkalin kotun Mai shari’a Adeniyi Ademola ya umarci lauyoyin bangarorin biyu su kammala tsarawa da musayar takardu kan shari’ar kafin wancan lokaci. Kuma kotun ta ba da umarnin a tsare wadanda ake tuhumar a Hukumar SSS har zuwa ranar da za a ci gaba da sauraren karar.