Kwartanci: Hisbah na neman Kwamishinan Jigawa ruwa a jallo
Ana zargin Kwamishinan da aka dakatar da mu’amala da matar aure.
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta ayyana Kwamishinan Harkoki na Musamman na Jihar Jigawa da aka dakatar, Auwal Danladi Sankara, a matsayin wanda ta ke nema ruwa a jallo.
Shugaban Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne, ya bayyana wa manema labarai cewa sun yi tsammanin Sankara zai amsa kiran fa hukumar ta yi masa, amma ya ƙi.
- Mun gano ƙwayoyi a gidan Sanata — NDLEA
- Ododo ya rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi a Kogi
Saboda rashin halartar kiran, Hisbah ta ayyana shi a matsayin wanda ta ke nema.
Daurawa, ya ce hukumar ta bayar da belin Kwamishinan ne bisa wasu sharuɗa.
“Aikinmu a Hisbah shi ne yin sulhu. Idan sulhu ya gagara, sai mu kai ƙara kotu.
“A wannan lamari, Nasiru Buba na zargin Sankara da yin mu’amala da matarsa. Mun kira ɓangarorin biyu don zaman sulhu, amma har yanzu Sankara bai bayyana ba,” in ji Daurawa.
Nasiru Buba, wanda ya shigar ƙarar, ya ce ya samu labarin cewa Sankara na ƙoƙarin samun umarnin babbar kotu don hana kama shi.
Ya roƙi Gwamnatin Jihar Kano da kuma Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, da su sa baki domin tabbatar da adalci.