Kwarya-Kwaryar Kasafin Kudin 2021: Wa Zai Amfana?
Gwamnati ta ce kwarya-kwaryar kasafin kudin da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu zai fara aiki nan take.
Shugaba Muhammadu Buhari yana sanya hannu a kan kwarya-kwaryar kasafin 2021
Gwamnatin Tarayya ta ce kwarya-kwaryar kasafin kudin 2021 da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu a ranar Litinin zai fara aiki nan take.
Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari a kan wadanda za su amfana da kasafin na sama da Naira biliyan 900.