Kwastam ne matsalar kasuwancinmu – ‘Yan Kasuwa
’Yan Kasuwar da ke sayar da bulawus-bulawus a Kasuwar kofar Wambai da ke birnin Kano sun koka game da yadda jami’an Kwastam ke kama musu kaya lamarin da kan jefa kasuwancin nasu cikin halin koma baya. Sakataren kungiyar ’Yan Masu Sayar da Bulawus-Bulawus (Blouse Sellers Association, Kano- BOSAK), Malam Sabi’u Yunusa shi ne ya bayyana […]
’Yan Kasuwar da ke sayar da bulawus-bulawus a Kasuwar kofar Wambai da ke birnin Kano sun koka game da yadda jami’an Kwastam ke kama musu kaya lamarin da kan jefa kasuwancin nasu cikin halin koma baya.
Sakataren kungiyar ’Yan Masu Sayar da Bulawus-Bulawus (Blouse Sellers Association, Kano- BOSAK), Malam Sabi’u Yunusa shi ne ya bayyana haka a yayin da yake zantawa da Aminiya a wannan mako, inda ya ce duk da kayayyakin da suke sayarwa na kasashen waje ne, amma ba su ne suke kawo kayan kai-tsaye ba.
“Duk da cewa ire-iren kayayyakin da muke sayarwa ba kaya ne namu na gida Najeriya ba; kaya ne da suke zuwa daga Dubai da Indiya da China, sai dai ba mu ne muke kawo kayan kai-tsaye ba, domin yawanci mukan same su ne daga Anaca da Legas. To a kan hanyar kawo kayan zuwa Kano ne muke matukar fuskantar matsala tsakaninmu da jami’an Kwastam. Haka suke kama mana kaya ba tare da yin la’akari da cewa ba mu ne muka shigo da kayan kai-tsaye daga kasashen wajen ba,” in ji shi.
Don haka sai Malam Sabi’u ya yi kira ga gwamnati musamamn a matakin tarayya ta tsawatar wa jami’an na Kwastam a kan hakan. “Koda a ce kayan nan suna cikin haramtattun kayayyaki da aka hana shigowa da su cikin kasa, bai kamata a ce an kwace mana kaya ba. Ina mamakin yadda kayan suke wuce jami’an Kwastam tun daga wurin shigowa da su, amma sai an zo kanmu masu karamin karfi sannan ne za a kama mana kaya.Don haka nake kira ga Gwamnatin Tarayya ta taimaka mana a kan wannan keta da ake yi mana”
Ya bayyana cewa kungiyarsu takan tallafa wa ’ya’yanta ta hanyoyi da dama musamman ma abin da ya shafi kasuwancinsu. “A duk lokacin da muka ga wani daga cikin ’ya’yan kungiyarmu ya shiga wani hali, kasuwancinsa yana fuskantar durkushewa, to kungiya takan yi ruwa-da-tsaki ta tallafa masa ta yadda zai ci gaba da harkokinsa na kasuwanci,” inji shi.
Malam Sabi’u ya ce hatta mutanen da ke wajenta ma sukan amfana daga tallafin kungiyar, domin a bara kungiyar ta tallafa wa akalla marayu 74 da kayan Sallah.
Har ila yau ya ce kungiyar tasu takan shiga ta yi sulhu tsakanin ’yan kasuwa, musamamn idan an samu wata rigima ta kudi. “Kasancewar yadda sha’anin kaswanci yake, za ki ga an samu rigimar kudi a tsakanin ’yan kasuwa a junansu ko ’yan kasuwa da masu ba su kaya daga waje, to, kungiyarmu takan yi kokari kwarai wajen sulhunta tsakaninsu. A yanzu ganin irin yadda muke kokari, ya sanya idan har rigimar kudi da ta shafi ’ya’yan kungiyarmu ta kai gaban ’yan sanda, to sukan dawo da batun wurinmu domin yin sulhu. Alhamdulillahi yawanci idan muka shiga cikin irin wadannan batutuwa ana samun nasarar yin sulhu,” inji shi.
A karshe ya nuna jin dadinsa game da hadin kai da goyon baya da ’ya’yan kungiyar ke bayarwa wajen ganin al’amura suna tafiya daidai yadda ya kamata a cikin kasuwar.