Kwastam sun kama Dala miliyan 8 a filin jirgin saman Legas

Jami’an Kwastan sun kama Dala miliyan 8 da dubu 65 da 615 da aka kudundune a cikin ambulan daban-daban a filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Legas. Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam ta Kasa, Kanar Hameed Ali (mai ritaya) ne ya bayyana haka a ranar Talata a Legas, lokacin da yake ganawa da manema […]

Kwastam sun kama Dala miliyan 8 a filin jirgin saman Legas

Jami’an Kwastan sun kama Dala miliyan 8 da dubu 65 da 615 da aka kudundune a cikin ambulan daban-daban a filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Legas.

Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam ta Kasa, Kanar Hameed Ali (mai ritaya) ne ya bayyana haka a ranar Talata a Legas, lokacin da yake ganawa da manema labarai.

Ya ce an kama kudin ne a cikin wata mota lokacin da ake kokarin sanya kudin a cikin jirgi. Sai dai kuma har yanzu ba a bayyana sunayen wadanda aka kama da kudin ba, sannan ba a fadi wane kamfanin jirgi ba ne da kuma inda zai je.

Amma Kanar Ali ya ce motar da aka kama kudin a cikinta, ta Kamfanin Kula da Zirga-Zirgar Jiragen Sama na Najeriya ne  (NAHCO).

Jaridar Premium Times ta ce wadanda ake zargin akwai direban da ya tuko motar, sai kuma wani ma’aikacin Kamfanin NAHCO da aka kama su kan zarginsu da laifin karkatar da kudi.

Ya ce “An nannade kudin a cikin ambulan, wadanda kowace aka rubuta sunan wanda za a kai wa kudin a matsayin kaya. Daga ranar da aka kama wadannan kudi har zuwa wannan lokaci babu wani banki da ya yi ikirarin cewa kudin nasa ne.”