Kwastam sun kama gurbataccen takin zamani
Rundunar Kwastam ta Seme a kan iyakar kasashen Najeriya da Benin ta yi nasarar kama buhunan gurbataccen takin zamani guda 900, wanda ke dauke da sinadarin da ke kona ciyayi da amfanin gona. Yanzu haka rundunar ta dukufa wajen yin binciken kwakwaf domin gano irin illar da wannan takin zamani mai guba zai iya haifarwa […]
Rundunar Kwastam ta Seme a kan iyakar kasashen Najeriya da Benin ta yi nasarar kama buhunan gurbataccen takin zamani guda 900, wanda ke dauke da sinadarin da ke kona ciyayi da amfanin gona. Yanzu haka rundunar ta dukufa wajen yin binciken kwakwaf domin gano irin illar da wannan takin zamani mai guba zai iya haifarwa idan aka yi kuskuren amfani da shi.
Da yake nuna wa ’yan jarida wadannan kaya a ofishinsa, Kwamandan Rundunar Kwastam ta Seme, Kwanturola Muhammed Aliyu Alhaji ya yi bayanin cewa, daga kasar Belarus aka yi odar shigo da gurbataccen takin, wanda wa’adin aikinsa ya kare a shekara ta 2015. Ya ce an yi satar shigo da kayan ne ta cikin kasar Benin da ke makwabtaka da Najeriya. “Wasu ’yan Najeriya masu kishin kasar haihuwarsu ne suka ba mu labari a boye, sai muka tura yaranmu suka kama wadannan kaya,” inji shi.
Da yake karin haske a kan irin illar da wannan gurbataccen takin zamani zai iya haifarwa sai ya ce: “Mun fara gano cewa wannan takin zamani yana dauke da guba ne a lokacin da wasu buhunan takin suka fashe a harabar shiga dakin ajiye kaya wanda bayan kwana uku duka ciyayin da takin ya zuba a kansu suka kone kurmus. A nan ne muka fara tunanin cewa watakila ana so a yi amfani da wannan takin zamani wajen harhada bama-bamai.”
Kwanturola ya ce ba a kama kowa da zargin shigowa da wannan kaya ba domin sun gudu. “Mun dauki tsauraran matakan gano tare da kama mutanen da suka yi odar shigowa da wannan kaya ta barauniyar hanya. Ka sani cewa shigowa da takin zamani kamar shigowa da motoci masu sulke ne, wadanda dole ne a nemi izini daga hukumar tsaro (NSA) kafin a shigo da su cikin kasa, domin ba a san abin da ake so a yi da irin wadannan kaya ba, inji shi.”
Ya ce, “matakin tsaurara matakan tsaro da sanya ido da Gwamnatin Tarayya ta dauka a kan shigowa da irin wannan takin zamani cikin kasa shi ne ya sa muka tashi tsaye wajen jajircewa da kyautata binciken kayan da ake shigowa da su ta wannan sashe tare da yin taka-tsan-tsan wajen lura da irin wannan kaya masu illa da ake kokarin shigowa da su cikin kasa.”
Ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da suka kama irin wannan kaya a kan iyaka ta Seme. “Kuma shi wannan takin zamani da muka kama, akwai alamar cewa an shigo da shi da mummunan nufi ne domin idan ka lura shi ne ya kona ciyayi cikin kwana uku da ya zube a cikin ciyayin. Saboda haka nake ganin cewa an shigo da shi ne domin ya kashe jama’a, ba domin ya taimake su ba ko kuma a ce an shigo da shi domin harhada bama-bamai.”
A game da irin matakin da jami’an kwastam suke dauka domin dakile ayyukan fasa kwauri, musamman a kan iyakar kasa da kasa ta Seme, sai Kwanturola Muhammad ya ce: “Ya kamata a tausaya wa jami’an Kwastam da suke yin sintiri a wannan yanki da a kullum daruruwan ’yan sumoga suke yin jerin gwano cikin motoci a cikin kungurmin dajin da ba za ka iya shiga ciki ba, inda suke yin dabarun shigowa da kayan da aka haramta shigowa da su cikin kasa.”
Dangane da nasarorin da rundunar ta samu, cewa ya yi duk da yake an samu karancin shigar kudaden shiga a dalilin dokar hana shigowa da motoci ta kan iyakoki, sai dai ya nuna wa ’yan jarida wasu kanana da manyan motoci da buhunan shinkafa da jarkokin man gyada da sudaddun tayoyin mota da suturun gwanjo da kayan lantarki na miliyoyin kudi da aka yi kokarin shigowa da su cikin kasa domin yin zagon kasa ga tattalin arzikin Najeriya.
Ya ce daga cikin buhunan shinkafa da suka kama sun aika da buhuna dubu 10 zuwa sansanin ’yan gudun hijira na Jihar Yobe a yayin da suke shirin lalata sauran shinkafar da wa’adin aikinta ya kare.