Kwastam sun kama haramtattun kayayyaki

Rundunar Kwastam ta FOU shiyya ta ‘A’ da ke Ikeja Legas ta kama buhunan rubabbiyar shinkafa buhu 1,300 da aka yi satar shigowa da ita cikin kasa domin sayarwa ga jama’a. Shinkafar, wadda aka kiyasta darajar kudinta a kan fiye da Naira miliyan 15, na daga cikin kamun kayayyaki da rundunar ta yi sau 54 […]

Kwastam sun kama haramtattun kayayyaki

Rundunar Kwastam ta FOU shiyya ta ‘A’ da ke Ikeja Legas ta kama buhunan rubabbiyar shinkafa buhu 1,300 da aka yi satar shigowa da ita cikin kasa domin sayarwa ga jama’a.

Shinkafar, wadda aka kiyasta darajar kudinta a kan fiye da Naira miliyan 15, na daga cikin kamun kayayyaki da rundunar ta yi sau 54 a tsakanin 9 zuwa 25 ga watan Agusta da ya gabata.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin Kwamandan rundunar, Kwanturola Muhammed Uba Garba, wanda ya jagoranci manyan mataimakansa zuwa nuna wa ’yan jarida irin kayan da suka yi nasarar kamawa a cikin wannan lokaci. Kayayyakin da aka kama sun hada da miyagun kwayoyi a cikin manyan motoci guda 2 da motocin alfarma masu tsada guda 27 da suturun gwanjo da aka cunkusa su a cikin daurin bel guda 137 da sababbi da sudaddun tayoyin mota da buhunan tabar wiwi da kayan lantarki.

Kwanturolan ya ce, an kama mutane 16 da ake zargin suna da hannu wajen shigowa da wadannan kaya ta filayen jiragen sama da tashoshin jiragen ruwa da kan iyakoki da ke cikin wannan sashe na Kudu maso yammacin kasa. Ya ce an kiyasta darajar duka kayan a kan Naira miliyan 783.

Da yake bayanin irin nasarorin da suka samu, ya ce: “A cikin watanni 3 da na fara aiki, mun yi gagarumar nasarar kama muhimman abubuwa da aka haramta shigowa da su cikin kasa. Wasu daga cikin irin wannan kaya ba a haramta shigowa da su ba amma sai ana yin amfani da su wajen boye miyagun kaya a cikin su. Wannan nasara da muka samu cikin wannan lokaci da na kama aiki ita ce ta sa Kwanturola-Janara Kanar Hameed Ali (mai ritaya) ya taso takanas daga Abuja zuwa nan Legas domin ya jinjina mana a kan irin ayyukan da muke yi na dakile yunkurin yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa da wasu marasa kishin kasa suke yi.

“Nasarar da muke samu ta biyo bayan matakin da Kwanturola Janar Hameed Ali ya dauka ne ta fannin wadata yaranmu da isasshen kayan aiki da horar da su sanin makamar aiki da biyan su albashi mai tsoka tare da kula da lafiya da rayuwarsu gaba daya. Haka kuma akwai wasu mutane masu kishin kasa da muke biyansu lada a kan labaran da suke samo mana a boye da suke taimaka mana kama irin wannan kaya. Ka san wannan aiki mu kadai ba za mu iya yinsa dari bisa dari ba, sai da taimakon jama’a har da ku ’yan jarida shi ne zai kai mu ga nasara.”