Kwastam sun kama makaman N1.6bn a filin jirgin Legas

An kama bindigogin Naira miliyan 270.8 da kuma jirage marasa matuka da kayan yaki da aka yi fasa-kwaurin su daga Turkiyya

Kwastam sun kama makaman N1.6bn a filin jirgin Legas

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama makamai da kudinsu ya haura Naira biliyan 1.6 a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Jihar Legas.

Makaman da aka kama sun hada da jirage marasa matuka da kakin soji da ragunan sulke da hulunan kwano da na’urorin sadarwa na oba-oba da sauran kayan yaki.

Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam na Kasa, Bashir Adewale Adeniyi, ya sanar cewa cikin makaman da aka kama akwai “bindigogi 55 masu sarrafa kansu kirar Jojef Magnum (Tomahawk) da kudinsu ya kai Naira miliyan 270.8.

“Bincikenmu ya gano cewa wasu ’yan Najeriya marasa kishi da ke zaune a kasar Turkiyya ne suka yi fasa-kwaurin makaman zuwa kasar nan.”

Ya kara da cewa an kama wani mutum da ake zargin hannunsa a shigowa da makaman da aka kama.

An yi wannan kamen ne a ranar Laraba, kimanin sa’o’i 48 bayan hukumar ta kama wata kwantaina makare da bindigogi 844 da harsasai 112,500 da aka yi fasa-kwaurin su zuwa Najeriya a tashar jiragen ruwa ta Onne a Jihar Ribas.

Shugaban kwastam na kasa ya bayyana cewa su ma makaman da aka kama a Jihar Ribas an yiwo fasa-kwaurinsu zuwa Najeriya ne daga kasar Turkiyya.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta