Kwastam sun kwace shinkafar waje da kwayar N2bn a Kano da Jigawa
A cikin wata biyu hukumar kwastam ta kwace shinkafar waje da miyagun kwayoyi da kayan gwanjo na kusan Naira biliyan biyu a Kano da Jigawa.
Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama shinkafar kasar waje da kayan gwanjo da miyagun kwayoyi da sauran haramtattun kaya kudin ya kai Naira biliyan 1.9 a cikin wata biyu a jihohin Kano da Jigawa.
Da yake bayanin haramattun kayan da hukumar ta kama bayan an yi fasa kwaurin ta daga kasar waje zuwa Najeriya, Kwanturolan Kwastam mai kula da shiyyar Kano da Jigawa, MA Umar, ya ce an kama kayan ne a tsakanin watan Maris da watan Afrilun 2022.
- ’Yan sanda sun ragargaji ’yan bindiga sun ceto mutum 15 a Neja
- Yi wa Su Dariye Afuwa Abu Ne Mai Sanyaya Guiwa —Lauyan EFCC
Umar ya bayyana wa manema labarai a ranar Talata cewa, “Mun kwace buhu 1,593 na shinkafar waje da aka yi fasa kwaurin ta, wadda kudinta ya kai Naira miliyan 46.7, sai kulli 275 na tabar wiwi da kuma kato bakwai na kwayar Tramadol.
“Sauran kayan sun ha da da katon 1,237 na sabulan kasar waje da kudinsu ya kai Naira miliyan 16.1 da katon 151 na taliya da dila 131 na tufafin gwanjo da kuma kati 34,940 na miyagun kwayoyi.
“Darajar kudin kayan da muka kama ta kai Naira biliyan daya da miliyan 966,” inji Kwantorulan.
A cewarsa, a cikin wata biyu, kudaden shiga da shiyyar ta samu sun karu zuwa Naira biliyan 14 daga Naira biliyan 9.6 da ta tara a baya.
Ya kuma bayyana cewa Hukumar Kwastam ta mika miyagun kwayoyi da aka kama ga Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) domin daukar matakin da ya dace a kansu.
Ya kuma gargadi jama’a da su guji ayyukan fasakwari domin suna gurgunta tattalin arziki; wadanda ba su daddara ba kuma za su yaba wa aya zaki.