Kwastam sun lakada wa yaron mota duka kan kin bayar da cin hanci
Wani yaron mota ya zargi wadansu jami’an Hukumar Kwastan da lakada masa duka kan kin ba su cin hanci. Yaron motar mai suna Aliyu Ahmed yana aiki ne da wata mota kirar J5 wadda ta dauko kayan bulawus daga Anaca zuwa Jos, kuma jami’an Kwastam din sun doke shi ne a dajin Forest da ke […]
Aliyu Ahmed da ake zargin kwastan sun yi wa duka
Wani yaron mota ya zargi wadansu jami’an Hukumar Kwastan da lakada masa duka kan kin ba su cin hanci. Yaron motar mai suna Aliyu Ahmed yana aiki ne da wata mota kirar J5 wadda ta dauko kayan bulawus daga Anaca zuwa Jos, kuma jami’an Kwastam din sun doke shi ne a dajin Forest da ke hanyar zuwa Jos a karshen makon jiya.
Da yake zantawa da wakilinmu Aliyu Ahmed ya ce sun taho daga Anaca zuwa Jos sai suka ga ana bin su a baya, ana ce su tsaya. Ya ce sai ya ce da direbansu ya tsaya, sai suka ga ashe jami’an Kwastan ne.
“Suka ce mu bude bayan mota suka fito da kayayyakin da muka dauko suka ga bulawus ne. Suka ce mu ba su takardar kayan, muka ba su. Suka duba sai suka ce mu kulle bayan motar. Suka ce suna son su yi magana da mai kayan. Sai muka kira musu Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Bulawus ta Kasuwar New Market da ke Jos, wadanda su ne masu kayan, muka gaya masa,” inji shi.
Aliyu Ahmed ya ce sai shugaban ya ce ba zai ba su komai ba, saboda manyan jami’an Hukumar ta Kwastan sun hana a rika ba su kudi.
Ya ce sai na ce musu idan suna zargin kayan ne su tafi da shi ofishinsu, idan kuma za su sallame mu ne, su taimaka su sallame su saboda gari yana wayewa. Ya ce daga wannan magana, sai wani daga cikinsu ya ce kada su yarda su gaya musu maganar banza. Wani cikinsu ya ce idan suka yi wasa za su yi musu dukan tsiya.
“Sai ni da maigidana muka ce me muka yi da za su yi mana duka. Ban gama rufe baki ba, sai wani ya cire dorina ya doke ni a kai. Ya kara kawo mini duka na biyu, sai na rike dorinar. Na ce masa me na yi kake dukana? Muna cikin haka sai sauran jami’an Kwastan din su hudu suka rufar mini, wani ya daga gindin bindiga ya buga mini a kai. Wani ya sake buga mini bindiga a kai. Daga nan na fadi kasa, suka ci gaba da buga mini sanda a kai. Daga baya haka sai suka zo suna ba ni hakuri. Suka kawo mini ruwa domin in wanke jikina saboda jinin da yake zuba. Na ce ba zan wanke jikina ba, domin sun zalunce ni,” inji shi.
Shugaban Kungiyar Masu sayar da Bulawus ta Kasuwar New Market da ke Jos, Alhaji Abubakar Isah Muhammad ya bayyana wa wakilinmu cewa rashin bai wa jami’an Kwastam din kudi ne ya haddasa wannan cin zarafi, “Kuma an dade ana yi mana irin wannan wulakancin daga wadansu jami’an Kwastam,” inji shi.
Sai ya yi kira ga Hukumar Kwastan ta Kasa ta yi bincike kan lamarin, domin a hukunta wadanda suke da hannu a ciki, saboda wannan gwamnati tana yaki da cin hanci da rashawa ne.
Amma a zantawarsa da wakilinmu kan al’amari, Kakakin Hukumar Kwastam ta Kasa, DC Josheph Attah ya ce abin da jami’ansu da suke aiki a waje suka ce sun tsare direban motar ce, ya ki tsayawa ya taho da gudu ya wuce.
Ya ce sun shiga mota za su bi shi, sai suka ga ya kauce daga hanya ya je ya fadi, sakamakon haka yaron motar ya samu raunuka a jikinsa. Ya ce direban bai tsaya ba balle jami’an su nemi ya ba su wani abu. Sai ya shawarci ’yan kasuwa da direbobin da suke dauko musu kayayyaki, su rika bin doka da oda.