Kwastam ta daina kwace kaya a kasuwanni — Sarkin Kano
Sarkin ya bukaci hukumar ta daga wa ‘yan kasuwa kafa.
Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya nuna jin dadi kan yadda aka samu fahimtar juna tsakanin ‘yan kasuwa da jami’an Hukumar Kwastam kan daina shiga kasuwanni tare da kwashe musu kaya.
Sarkin, ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakuncin shugaban hukumar na kasa, Bashir Adewale Adeniyi a fadarsa da ke Kano.
- Gobara: An ceto mutum 6 da dukiyar miliyan 107 a Kano
- ’Yan bindiga sun sace ɗaliban Tsangaya a Sakkwato
Sarkin ya ce a baya sun sha karbar korafe-korafen ‘yan kasuwa kan yadda jami’an hukumar ke shiga kasuwanni suna kwashe musu kaya.
Kazalika, Sarkin ya bukaci Babban Kwanturolan hukumar, idan za su raba kayan abinci da su duba mabukata, musamman ta hanyar neman hadin kan masarautun gargajiya.
A nasa jawabin shugaban hukumar, Bashir Adewale Adeniyi, ya ce ya kai ziyarar ne domin neman shawarwari da kuma hanyoyin inganta ayyukansu.
Shugaban, ya samu rakiyar shugabn hukumar na shiyyar Kano da Jigawa, Dauda China da kuma manyan jami’an hukumar.