Kwastam ta gargadi ‘yan sumogal kan kisan jami’anta

Hukumar Kwastan ta Kasa a Jihar Kano ta gargadi ’yan sumoga su shiga taitayinsu a kan hallaka jami’anta da suke yi. Kakakin Hukumar ta Jihar Kano da Jigawa, Alhaji Isa Danbaba ya shaida wa Aminiya cewa kasancewar hukumar tana farautar ’yan sumoga masu shigowa da haramtattun kayayyaki cikin jihar ya sa su kuma suka bullo […]

Kwastam ta gargadi ‘yan sumogal kan kisan jami’anta
Kwastam ta gargadi ‘yan sumogal kan kisan jami’anta

Hukumar Kwastan ta Kasa a Jihar Kano ta gargadi ’yan sumoga su shiga taitayinsu a kan hallaka jami’anta da suke yi. Kakakin Hukumar ta Jihar Kano da Jigawa, Alhaji Isa Danbaba ya shaida wa Aminiya cewa kasancewar hukumar tana farautar ’yan sumoga masu shigowa da haramtattun kayayyaki cikin jihar ya sa su kuma suka bullo da salon hallaka jami’anta ta hanyar buge su da mota.

“Masu sumoga musamman wadanda ke shigowa da motoci da aka fi sani da tokumbo sun bullo da wani salo na hallaka jami’anmu inda suke bin jami’anmu da gangan suna buge su da mota. A yayin da wasu lokuta jami’an namu sukan samu raunuka wadansu kuma sukan samu kansu a kabari. Irin haka ta faru a ranar Lahadin da ta gabata inda wadansu ’yan sumoga masu shigo da motoci suka biyo jami’inmu a guje mai suna Musa T. Y suka buge shi. Hakan ya jawo kafarsa ta karye, bayan an kai shi asibiti aka gano ya samu kwanciyar jini a cikinsa, daga baya kuma ya rasu,” inji shi.

Kakakin Kwastam din ya ce ba wannan ne karo na farko ba domin a kwankin baya irin haka ta faru inda wadansu ’yan sumoga suka hallaka wani jami’in hukumar.

Hukumar ta nanata cewa ba za ta ci gaba da zuba idanu ana kashe mata jami’anta kamar tumaki ba, don haka za ta dauki matakin murkushe duk wani mai kokarin yi wa hukumar shiga hanci da kudundune.

Alhaji Danbaba ya yi kira ga jama’a su bi doka domin a zauna lafiya “Ya kamata jama’a su fahimci cewa wannan aiki da Kwastam ke yi, suna yin sa ne bisa doka ba suna yi ne don cin mutuncin wani ko don ganin bayan wani ko kuma don a karya wani ba, an kawo su ne don a samu gyara tattalin arzikin kasa,” inji shi