Kwastam ta hana shigo da motoci ta iyakokin kasa
Gwamnatin Tarayya ta hana shigo da motoci ta kan iyakarta ta kasa daga ranar 1 ga watan Janairun sabuwar shekara. A wata sanarwa da Hukumar Kwastam ta fitar ranar Litinin, ta ce ta haramta shigo da tsofaffin da kuma sababbin motoci.Haramcin yana zuwa ne bayan hana shigo da shinkafa ta iyakokin kasa da gwamnatin ta […]
Gwamnatin Tarayya ta hana shigo da motoci ta kan iyakarta ta kasa daga ranar 1 ga watan Janairun sabuwar shekara.
A wata sanarwa da Hukumar Kwastam ta fitar ranar Litinin, ta ce ta haramta shigo da tsofaffin da kuma sababbin motoci.
Haramcin yana zuwa ne bayan hana shigo da shinkafa ta iyakokin kasa da gwamnatin ta dauka a watan Afrilun da ya gabata. Matakin ya takaita shigo da shinkafa ne kawai ta iyakokin ruwa.
Hukumar hana fasa kaurin ta kuma shawarci maso shigowa da motoci ta kasa da su gaggauta kwashe motocin da suka shigo dasu a ruwa, amma kuma suke wasu tashoshin jiragen ruwa na wasu kasashe makwabta.
A watan Oktoba ne Shugaban Hukumar Kwastam Kanar Hameed Ali ya ce fadar shugaban kasa tana shirin hana shigo da motoci ta iyakokin kasa. Ya ce hakan zai magance ayyukan fasa kaurin da ake yi ta iyakokin kasar nan ta kasa.