Kwastam ta kama buhu 707 na shinkafar waje a Kano
Hukumar ta kuma kama kayan miliyan 41.3 da aka yi fasakwaurinsu
Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama buhu 707 na shinkafar waje da aka yi fasakwaurin ta a Jihar Kano.
Ofishin Hukumar Kwastam mai kula da shiyyar Jigawa da Kano ya ce jami’an hukumar sun kwace shinkafar wajen ne gami da wasu kayayyakin da aka yi fasakwaurinsu wadanda kimar kudadensu ta kai Naira miliyan 41.3 daga watan Yuli zuwa Satumba.
- Ana binciken masu satar bayanan sirri su yada a kafafen sada zumunta
- Ba za mu fallasa masu taimakon ’yan ta’adda ba —Gwamnati
Da yake sanar da hakan a Kano, Kwamandan shiyyar, Suleiman Umar, ya ce “Ina kara fada da babbar murya cewa doka ta ba wa hukumar kwastam ikon binciken duk wuraren da ake boye kayan da aka yi fasakwaurin su.
“Dokar da ta kafa hukumar kwastam ta kuma ba mu ikon yin sintiri da tsare duk wanda ya kamata domin tabbatar da dokoki da tsare-tsaren kudin gwamanti’’.
A cewarsa, sauran kayan da hukumar ta kama bayan shinkafar wajen sun hada da dila 155 na kayan gwanjo, kwalayen taliya 130, jarka 16 na man girki, kwalayen madara 231, makaroni kwali takwas, kwali 30 na maganin sauro na hayaki, katon 10 na batura da kuma katon shida na angur da aka sarrafa a kasar Ghana.
Ofishin shiyyar, a cewarsa, ya tara Naira biliyan 16.9 daga watan Janairu zuwa watan Agustan shekarar 2021 da muke ciki.