Kwastam ta kama jirage marasa matuƙa 148 a Legas
An kuma kama jabun dalar Amurka miliyan daya da dubu dari biyu da hamsin a filin jirgin saman Legas.
Hukumar Hana Fasakauri ta Nijeriya wato Kwastam ta kama wasu jirage marasa matuƙa guda 148 da kuɗinsu ya kai kimanin naira miliyan bakwai da kuma injina na harkokin kuɗin intanet (crypto currency) guda biyar.
Hukumar ta kama waɗannan kayayyaki da kuma jabun dalar Amurka miliyan daya da dubu dari biyu da hamsin ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Jihar Legas.
Shugaban Hukumar Kwastam shiyyar Legas ya mika wadannan kayayyaki ga Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Ta’annati (EFCC) da Rundunar Sojin Najeriya.
Da yake jawabi yayin mika jabun dalar ga shugaban EFCC a Jihar Legas, kwantirola Charles Orbih ya ce, “ga wadannan jabun dalar Amurka har ta miliyan daya da dubu dari biyu da hamsin, ga kuma injina na harkokin kuɗin intanet guda biyar.
“Mai yiwuwa wasu su ga cewa wadannan kayayyakin ba su taka kara sun karya ba, amma abin da ya kamata kowa ya sani shi ne, za su iya yi wa tattalin arzikin Najeriya mummunar illa.”
- Sojoji Sun Mika ’Yar Chibok Da Aka Ceto Da Yara 3 Ga Gwamnatin Borno
- Dan Majalisar Tarayya daga Jigawa ya rasu
A nasa jawabin, wakilin mukaddashin shugaban hukumar EFCC a yankin Legas, ya jinjinawa hukumar Kwastam bisa wannan namijin kokari.
“A madadin shugaban hukumar EFCC ta Najeriya, da mukaddashin shugaban hukumar a yankin Legas, ina jinjina muku kwarai da gaske.
“Wannan kokari da kuke yi zai taimaka wurin tsaftace al’ummarmu domin mu mori rayuwa a cikin aminci, kuma yana saukaka mana aikinmu.”
Kwantirolan Hukumar Kwastam din ya mika jirage marasa matukan guda 148 ga Manjo Janar Muhammad Usman na rundunar sojin Najeriya.
Kwantirolan ya ce, “wadan nan na’urori na (drone) suna da tsari da ingancin na tsayuwar tsawon awa 72 a sararin samaniya.
Shi ma a nasa bangaren, Manjo Janar Muhammad Usman ya jinjina wa hukumar ta Kwastam, ya kuma yaba wa jajircewarta.
“Irin wannan kokari na hadin gwiwa zai taimaka wurin tabbatar da fatan shugabannin hukumomin tsaron kasar nan na ganin ana aiki tsintsiya madaurinki daya.”
Ya mika godiya ga hukumar ta Kwastam, ya kuma ba ta tabbacin goyon baya wurin ci gaba da inganta harkokin tsaro a Najeriya.