Kwastam ta kama kayan abinci na naira miliyan 30 a Kano
Hukumar hana fasa kwari ta Najeriya shiyyar Kano da Jigawa ta yi nasarar kama kayan abinci da ya kai na sama da naira miliyan 30 a jihar Kano kamar yadda kwantirolan Hukumar na jihar Nasir Ahmad ya sanar. A lokacin da Ahmed yake ganawa da manema labarai a Kano ya bayyana cewa, sun kama buhunan […]
Hukumar hana fasa kwari ta Najeriya shiyyar Kano da Jigawa ta yi nasarar kama kayan abinci da ya kai na sama da naira miliyan 30 a jihar Kano kamar yadda kwantirolan Hukumar na jihar Nasir Ahmad ya sanar.
A lokacin da Ahmed yake ganawa da manema labarai a Kano ya bayyana cewa, sun kama buhunan shinkafar waje 1,200 da kudinsu ya kai Naira 26,863,200, da mangyada lita 25 jarka 300 da kudinsu ya kai Naira 3,476,340, sigari ta waje buhu 100 da kudinsu ya kai naira 2,178,500 da kuma taliyar sapageti katan 200 da kudinsu ya kai 402,620.
Ahmad ya ce an shigo da kayan ne ta barauniyar hanya zuwa jihar ta hanyoyin Daura, Gwarzo, Bichi da Babura. Akalla motoci 14 suka yi jigilar kayan.