Kwastam ta kama kayan sojoji da ƙwayar N31bn

Ɗaya daga cikin kwantainonin yana ɗauke ne da seti 4,800 na kayan yaƙin sojoji da takalma da rigunan ruwand sauransu

Kwastam ta kama kayan sojoji da ƙwayar N31bn

Wasu miyagun kwayoyi da NDLEA ta kama.

Jami’an Kwastam sun kama kwantainoni makare da kayan yaƙin sojoji da miyagun ƙwayoyi ƙimarsu ta kai Naira biliyan 31 a Tashar Jiragen Ruwa ta Onne da ke Jihar Ribas.

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce jami’anta sun kama kwantainoni 12 ɗauke kayan sojoji da miyagu ƙwayoyin ne bayan haɗin gwiwar jami’an tsaro.

Shugaban Hukumar Kwastam Bashir Adawale Adeniyi, ya ce ɗaya daga cikin kwantainonin yana ɗauke ne da seti 4,800 na kayan yaƙin sojoji da takalma da rigunan ruwa da sauransu guda 67,320.

Kwantainoni 11 kuma ɗauke suke da kwalabe 1,734,400 na maganin tari na ruwa mai ɗauke da kodin da kwaya 24,480,000 na Royal Tramadol Hydrochloride, da kuma Tapentadol and Carisoprodol guda 5,350,000.

Akwai kuma Really Extra Diclofenac guda 1,300,000 da kuma kwaya 7,250,000 ta Trodol Benzhexol a cikinsu.

Shugaban na kwastam ya bayyana damuwa cewa an kama waɗannan kayan sojojin ƙwayoyi ne, bayan a kwanan baya hukumar ta kama makaman da aka shigo da su Najeriya ba bisa ka’ida ba a tashar jiragen ruwan.

Ya ce wannan babbar barazana ce da ke buƙatar a kara dagewa domin hana wa masu yi wannan muguwar harka ruwa gudu.

Don haka ya roki jama’a da su taimaka su ci gaba da tsegunta wa jami’an tsaro game da ayyukan bata-gari domin a daƙile su kafin su yi wa al’umma illa.

Ya ce Kwastam za su miƙa wa Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ƙwayoyin da aka kama.

Kayan sojojin da sauran laifin kuma za a miƙa su ga hukumomin da suka dace kamar yadda doka ta tanada.

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato