Kwastam ta kama man fetur na Naira miliyan 8.8 a Legas

An ɓoye man fetur ɗin a cikin ganga 61, inda kowace ganga ke ɗauke da lita 25 ta man fetur.

Kwastam ta kama man fetur na Naira miliyan 8.8 a Legas

Hukumar Kwastam ta sanar da samun nasarar kama man fetur da darajarsa ta kai kusan Naira miliyan 8.85 daga hannun masu fasa ƙwauri a Legas a yayin da ake fama da ƙarancinsa a ƙasar.

A cewar Kwanturola Paul Bamisaiye, kwamandan hukumar ta Kwastam na shiyyar Yamma, an tsananta sintiri a magudanan ruwa a Legas, lamarin da ya sa aka kama man fetur ɗin da aka yi fasa ƙwaurinsa, wanda ake daf da ƙetarewa da shi zuwa Jamhuriyar Benin.

Bayanai sun ce an ɓoye man fetur ɗin da aka ɓoye a cikin ganga 61, inda duk ganga ke ɗauke da lita 25 na man fetur.

Jami’an sun yi nasarar kama man ne a kan tekun Isalu Creek-Badagry da ya ratsa ta hanyar zuwa Jamhuriyar Benin.

Da yake jawabi ga manema labarai, Bamisaiye ya jaddada mahimmancin kamen, musamman a lokacin da ake fama da ƙarancin man fetur, musamman a manyan biranen ƙasar.

 Ya yaba da matakan da jami’an suka ɗauka don daƙile ayyukan masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa.

Aminiya ta ruwaito cewa an kama masu aikata laifin ne biyo bayan sahihan bayanan sirri da rundunar ta samu, lamarin da ya sa jami’an sintiri suka mayar da martani cikin gaggawa.

Sai dai ababen zargin sun tsere sun bar kwale-kwalen da aka yi lodin man fetur ɗin, yayin da jami’an na kwastam suka garzaya da shi reshensu da ke Badagry domin gudanar da bincike.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda